Sojoji za su fara tura mutum-mutumin ‘Robots’ domin su yaki ‘Yan ta’adda a Najeriya
- Sojojin Najeriya suna shirin kirkiro na’urorin da za su taimaka wajen yakar matsalar rashin tsaro.
- Hukumomin NITDA da NCAIR ne za su taimakawa jami’an tsaron wajen cin ma wannan burin na su.
- Shugaban NACEST, Janar Yahaya H Abdulhamid ya kai wa shugaban NCAIR ziyara a kan batun
Benue - Sojojin Najeriya na kokarin komawa amfani da mutum-mutumi watau Robots da sauran na’urorin kimiyya da fasaha wajen magance rashin tsaro.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa hukumar NITDA da NCAIR za su hada-kai domin kirkiro sababbin hanyoyin da za a shawo kan matsalar tsaro a kasa.
Wadannan hukumomi da ke kawo cigaba ta fuskar fasahar IT da kuma kirkire-kirkiren mutum-mutumi za su bada gudumuwa wajen kawo zaman lafiya.
Rahoton ya ce wannan yunkuri da za a yi zai taimaka sosai wajen samar da bayanan da suka danganci sha’anin tsaro ta hanyar cin moriyar fasahar zamani.
Shugaban hukumar NCAIR na kasa, Injiniya Ya’u Garba Isa ya bayyana wannan a lokacin da ya gana da shugaban makarantar sojoji ta NACEST a Benuwai.
Shugaban NACEST, Birgediya Janar Yahaya H Abdulhamid ya kai wa Injiniya Ya’u Isa ziyara a ofishinsa da ke birnin Makurdi, Benuwai a ranar Alhamis.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
NITDA, NCAIR za su taimakawa sojoji
A jawabin da Isa ya fitar, yace za su hada-kai da sojoji domin kirkiro na’urorin da za su yaki miyagu.
Shugaban hukumar yace an kafa NCAIR ne domin bincike da kirkiren zamani, tana yin aiki ne fasahar AI, mutum-mutumi da IOT, da sauran cigaba na Duniya.
Sahara Reporters tace za a tura wadannan robots masu kama da mutane zuwa filin yaki domin su kawo karshen ‘yan ta’adda, da duk wasu miyagun ‘yan bindiga.
“NCAIR na kokarin samar da kirkire-kirkire, salon kasuwancin zamani, samar da aikin yi, da kawo cigaban kasa.”
Cibiyar za ta duba yiwuwar samar da bam na komguta da zai yi aiki da fasahar WLAN a fagen fama.” - Ya’u Isa
Kasafin 2022: N570bn ba za su ba - COAS
A makon nan ne shugaban hafsun Sojoji, Janar Farouk Yahaya ya sanar da Sanatoci cewa kudin da aka warewa Rundunar Najeriya a kasafin 2022 sun yi kadan.
Abin da sojoji za s kashe a shekara mai zuwa ba zai zarce N570bn ba. A halin yanzu Najeriya tana fama da ‘Yan ta’adda, ‘Yan bindiga da kuma masu tada kayar baya.
Asali: Legit.ng