Borno: Hukumar EFCC ta kama Mamman Shuwa da ya sayarwa mutane 3 wani filin gwamnati guda ɗaya
- Hukumar yaki da rashawa ta EFCC, ta gabatar da Mohammed Gapchia-Gana wanda aka fi sani da Mamman Shuwa gaban Alkali bisa damfarar mutane 3 ta hanyar sayar mu su da filin gwamnati
- Ya amshi N850,000 a hannun Muhammad Hassan, Fatima Buba N700,000 sai Falmata N650,000, duk a kan filin guda daya da ke kan titin Damboa a cikin Maiduguri
- Shugaban yada labaran hukumar EFCC, Mr Wilson Uwujaren a wata takarda ya ce gaskiya ta bayyana ne bayan hukumar kula da gine-ginen jihar Borno ta rushe ginin da daya daga cikin wadanda ya siyar wa wurin ya fara
Borno - Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta gabatar da Mohammed Gapchia-Gana wanda aka fi sani da Mamman Shuwa gaban alkali Aisha Kumaliya ta babbar kotun jihar Borno da ke Maiduguri akan laifuka 3, na damfara, cuta da yaudara.
Kamar yadda EFCC ta wallafa a shafinta na Facebook, ya sayar wa Mohammed Hassan, Fatima Buba da Falmata Fali wani fili da ke titin Damboa a Maiduguri wanda na gwamnati ne.
Ya amshi N850,000 daga hannun Hassan, N700,000 daga Buba sai N650,000 daga hannun Fali duk a kan fili daya kamar yadda ya zo a sanarwar ta EFCC.
Shugaban yada labaran EFCC, Mr Wilson Uwujaren, a wata takarda ya ce an gano gaskiya ne bayan daya daga cikin wadanda ya sayar ma wa ya fara gini sai hukumar kula da gine-ginen jihar Borno ta rushe filin tunda na gwamnati ne.
Hakan ya sa wadanda ya sayar wa filin su ka kai korafi akan Gapchia-Gana.
Kamar yadda wani bangare na takardar ya nuna:
“An gano yadda kai, Mohammed Gapchia-Gana wanda aka fi sani da Mamman Shuwa, a watan Disamban 2018 a birnin Maiduguri jihar Borno, da niyyar damfara ka siyar wa Mohammed Hassan wani fili da ke 44G, kusa da ofishin ‘yan kwana-kwana wurin titin Damboa a N850,000.
“Ka yi hakan bisa ganganci da yaudara, laifin da ya ci karo da bangare na 1(1) na dokar damfara ta 2006, kuma hukuncin na bangare na 1(3) na dokar.”
Wanda ake zargin ya ki amsa laifukan da ake zargin sa da shi
Kamar yadda takardar ta nuna, wanda ake zargin ya ki amsa laifuka 3 da hukumar ta ke zargin sa da aikatawa.
Lauyan mai kara, Fatima Muhammad ta bukaci kotu da ta dage karar kuma ta kulle wanda ake zargin.
Alkali Kumaliya ta dage sauraron karar zuwa ranar 29 ga watan Nuwamban 2021 don ci gaba da sauraron shari’ar kuma ta bukaci ya kulle wanda ake zargin.
Kotu ta ɗaure wani matashi da ya yi asubanci ya tafi coci ya sace kujerun roba
A wani rahoton, wata kotun majistare ta daure wani matashi, Lekan Alaka, mai shekaru 19, watanni 3 bisa satar kujerun roba masu kimar N91,200 daga cocin Mount Zion Angelican.
‘Yan sandan sun kama Alaka da laifin sata kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Alkali Olajumoke Somefun ya yanke hukunci bisa tabbatar da laifin da ya aikata bisa ruwayar Vanguard.
Asali: Legit.ng