Bayan kwana 3 a hannun EFCC, Obi Cubana ya cika sharuddan beli, an sako shi
- Hukumar EFCC ta saki fitaccen biloniya, Obi Cubana, bayan kwashe kwanaki uku a hannun ta
- An gano cewa, bayan titsiye shi da jami'an hukumar suka yi, sai a yammacin Alhamis ya cika sharuddan beli
- Kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da cewa a yammacin Alhamis suka sako biloniyan
Abuja - Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta bayar da belin fitaccen biloniya, Obinna Iyiegbu wanda aka fi sani da Obi Cubana.
Dan asalin jihar Anambran kuma mamallakin mashaya, ya isa hedkwatar hukumar ne da ke Jabi a Abuja ranar Litinin da rana amma sai yammacin Alhamis aka sako shi, Daily Trust ta tabbatar.
Zargin da ake yi wa biloniyan har yanzu an ki bayyanawa, sai dai wani babban jami'in hukumar ya ce akwai halasta kudin haram da kuma zambar haraji daga cikin laifukansa.
Daily Trust ta gano cewa, bayan titsiye shi da jami'an hukumar suka yi, ba su bar shi ya tafi gida ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wilson Uwujaren, mai magana da yawun hukumar EFCC ya tabbatar wa da Daily Trust cewa an sako shi sai dai ba cigaba da bayar da bayani ba.
"Tabbas, an sake shi da yammacin nan na Alhamis," Uwujaren yace a saukake.
Obi Cubana ya shiga kanun labarai a watan Yuli bayan ya zubar da ruwan kudi yayin birne mahaifiyarsa a Oba, jihar Anambra inda aka yanka sama da shanu dari biyu.
Asali: Legit.ng