Miyagun yan bindiga sun bi tsakar dare sun yi awon gaba da mata zalla a Neja
- Hukumar yan sanda reshen jihar Neja ta bayyana cewa wasu yan bindiga sun yi awon gaba da mata huɗu a yankin karamar hukumar Suleja
- Kwamishinan yan sandan jihar, Monday Kuryas, yace maharan sun farmaki kauyen ne da tsakar daren Laraba
- Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa yan bindigan sun buɗe wuta da zuwansu domin tsorata mutanen ƙauyen
Niger - Rundunar yan sandan jihar Neja, a ranar Alhamis ta tabbatar da sace mata huɗu da wasu tsagerun yan bindiga suka yi a ƙauyen Haske Dabara, yankin karamar hukumar Suleja.
Kwamishinan yan sandan jihar, Mista Monday Kuryas, shine ya bayyana haka a wata hira da hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) a Minna.
The Nation ta rahoto cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na daren ranar Laraba da ta gabata.
Sai dai wani shaidan gani da ido, yace maharan sun shigo ƙauyen ne da misalin karfe 12:46 na dare, inda suka buɗe wuta domin tsorata mutane.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yaushe aka sace matan?
Leadership ta rahoto kwamishinan yace:
"Eh tabbas lamarin ya faru da misalin karfe 1:00 na daren ranar Laraba kuma tuni hukumar yan sanda ta tura jami'ai masu yaƙi da garkuwa, sojoji da yan Bijilanti domin ceto waɗan da aka sace."
"Zamu yi iyakar bakin kokari mu kame duk wanda ke da hannun wurin hana al'umma zaman lafiya."
"Ina rokon jama'a, musamman na yankin karkara, su daina jin tsoro wajen taimaka mana da bayanai kan duk wani da basu gane ba a cikinsu, su faɗa mana a caji ofis mafi kusa."
Muna bukatar taimakon al'umma
Kwamishinan ya jaddada bukatar da jami'an tsaro ke da shi daga wurin mutane, na basu bayanai domin samun sauki a kokarin da suke na magance satar mutane, fashi da makami da sauransu.
A wani labarin kuma Rikici ya barke tsakanin yan Keke-Napep da jami'an yan sanda, An bindige mutum daya
Yanzun haka direbobin Keke-Napep na can suna zanga-zanga a yankin Abule-Egba dake jihar Legas bisa zargin jami'an yan sanda da harbe ɗaya daga cikinsu.
Wasu na zargin cewa jami'in hukumar yan sanda ne ya daba wa direban Keke-Napep ɗin wuka yayin da wasu ke cewa bindige shi ya yi, kuma ya barshi nan kan hanya har ya mutu.
Asali: Legit.ng