An gano an yi kuskure bayan shekaru 22 da jefa mutum Kurkuku, an bashi N9bn ya rage zafi
- A shekarar 1994, kotu ta damke wani mutumi mai suna Eddie Bolden da laifin kashe mutum biyu a kasar Amurka
- Bayan shekaru 22 da ya kwashe a gidan gyaran hali aka tabbatar da cewa lallai kuskure akayi bai aikata laifin ba
- A 2016 aka sakeshi kuma ya shigar da kara kotu bisa zaluncin da akayi masa, kotu tace a biyashi bilyan tara
Amurka - Wani mutum dan shekara 51 ya fashe da hawayen farin ciki bayan an wankeshi daga laifin da aka zargeshi da aikatawa kuma aka jefashi kurkuku shekaru 22.
Tun 1994 da aka jefasa gidan maza, dan kasar Amurkan mai suna Eddie Bolden, ya samu fitowa a shekarar 2016 bayan fafatawa da lauyoyinsa sukayi tsawon shekaru biyu a kotu, CBS News ta ruwaito.
Fitowarsa ke da wuya, Eddie ya maka gwamnatin Chicago kotu kan zaman kurkukun da yayi shekaru 22.
Chicago Sun Time ta ruwaito cewa bayan kwashe lokaci ana zaman kotu, an yanke hukuncin cewa a biyashi N9,923,291,764 ya rage zafi.
Hakazalika kuma aka bashi takardar shaidar wankeshi daga laifukan kisan mutum biyu da akayi masa.
Hukuncin kotun
A hukuncin da kotu ta yanke, ta umurci gwamnatin Chicago ta biya Bolden N9,923,291,764 matsayin diyya kuma jami'an yan sandan da suka daura masa laifin su biyashi N4,042,822.
Bolden yace sun daura masa laifin kisa matasa Irving Clayton da Derrick Frazier.
Lauyan Bolden ya bayyanawa kotu cewa babu wata hujja da ta nuna shi ya aikata laifin kawai dai an kamashi ne saboda bakin fata ne.
Kano: An gurfanar da wanda ya kira Ganduje 'ɓarawon Kano' a Facebook, kotu ta bada umurnin tsare shi
Kotu ta yanke wa tsohon manajan banki shekaru 8 a gidan yari kan satar N219m a banki
A gida Najeriya kuwa, wata babbar kotu da ke zamanta a jihar Enugu ta yanke wa tsohon manajan wani banki shekaru 8 saboda sata da almundahana.
Jaridar Independent ta ruwaito yadda alkalin kotun, Justice Cyprain Ajah ya yanke wa Mr Anidiobi Chukwuka hukuncin bayan EFCC ta zarge shi da laifuka 32.
An gabatar da manajan bankin gaban kotu bisa ruwayar The Punch bayan zargin sa da sata da mayar da kudin wani na amfanin sa.
An samu bayanai akan yadda ya yashe N219,000,000 daga asusun wani kwastoma bayan ya adana kudin a bankin.
Asali: Legit.ng