Shugaban NDLEA: Ba kudi a hukumar NDLEA, daga gidana na dauko TV zuwa ofis

Shugaban NDLEA: Ba kudi a hukumar NDLEA, daga gidana na dauko TV zuwa ofis

  • Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya), ya yi korafi a kan rashin warewa hukumar isasshen kudi don gudanar da ayyukanta
  • Marwa ya bayyana cewa daga gidansa ya dauko TV zuwa ofis a lokacin da ya kama aiki a matsayin shugaban hukumar
  • Ya yi kira ga majalisa a kan ta taimaka wajen ganin an warewa hukumar isasshen kudi domin aiwatar da ayyukanta cikin nasara

Abuja - Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA), Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya), ya koka kan rashin isasshen kudi a hukumar.

Marwa ya bayyana cewa a lokacin da ya kama aiki a matsayin shugaban hukumar, daga gidansa ya dauko talbijin zuwa ofis, rahoton Daily Trust.

Shugaban NDLEA: Ba kudi a hukumar NDLEA, daga gidana na dauko TV zuwa ofis
Shugaban NDLEA: Ba kudi a hukumar NDLEA, daga gidana na dauko TV zuwa ofis Hoto: Punchng.com
Asali: UGC

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 3 ga watan Nuwamba, a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisa kan miyagun kwayoyi domin kare naira biliyan 38 na kasafin kudin hukumarsa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Wani gini mai hawa-hawa ya sake ruftawa a jihar Legas

Shugaban na NDLEA ya ce rashin kudi shine babban koma baya ga ingantaccen ayyukan hukumar mai shekaru 32.

Marwa ya fada ma kwamitin cewa hukumar wacce ke da karfin ma'aikata 10,000 da sansanoni 173 a fadin kasar baya ga hedkwata, tana samun naira miliyan 33 duk wata don gudanar da ayyukanta.

Wani nazari na kwatankwacin kudaden da wasu hukumomin tarayya ke samu a bisa ga wata takarda ya nuna cewa hukumomi irin EFCC mai karfin ma'aikata 2,800 tana samun miliyan 300 duk wata don gudnar da ayyuka.

Hukumar ICPC mai karfin ma'aikata 800 tana samun miliyan 151 duk wata, NFIU da ma'aikata 500 tana samun miliyan 75 yayin da NDLEA mai ma'aikata 10,000 ke samun miliyan 33 duk wata.

Ya ce rashin isasshen kudi a hukumar zai shafi kokarinta wajen yaki da miyagun kwayoyi yadda ya kamata da kuma illolin da ke tattare da shi ga tsaron kasa.

Kara karanta wannan

Kasafin 2022: Ta kacame tsakanin sanatoci kan raba wa mazabu ayyukan tituna

Ya bukaci kwamitin majalisar da ya tallafawa hukumar wajen ganin an samu ci gaba ta fuskacin samar da kudade domin magance muhimman abubuwan da hukumar ke bukata domin inganta aiki.

Shugaban kwamitin majalisa kan miyagun kwayoyi, Dr Francis Ottah Agbo, yayin da yake yaba ma kokarin Marwa a yaki da miyagun kwayoyi a kasar, ya bayar da tabbacin cewa za su tattauna da shugaban kwamitin kasafin kudi.

Ya ce za su tabbatar da samar da ingantattun kudade ga hukumar domin habbaka ayyukanta.

Rahoton ya kuma nuna cewa kwamitin ya gayyaci dan kwangilar da ke kula da ginin NDLEA ke yi a hanyar titin filin jirgin sama na Abuja da ya bayyana a gabansa domin ya yi bayani kan dalilin jinkirin da aka samu wajen kammala aikin.

NDLEA ta cika hannu da wani dillalin Miyagun Kwayoyi Da Hodar Iblis Na N2.3Bn a Abuja

A wani labarin, hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta kama wani mai suna Okey Eze, kasurgumin dillalin miyagun kwayoyi a filin sauka da tashin jirage na Nnamdi Azikiwe, Abuja.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Matasa sama da 172 sun haukace a jihar Zamfara

An damke Eze dauke da nadi 350 na hodar Iblis wanda kudin sa ya kai Naira biliyan biyu da digo uku (N2.3bn).

Hadimin shugaban hukumar, Mahmud Isa Yola, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Laraba, 22 ga Satumba, 2021.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng