Borno: ISWAP ta sako manoma 76 da ta kama, ta yi musu bulala kafin sakinsu

Borno: ISWAP ta sako manoma 76 da ta kama, ta yi musu bulala kafin sakinsu

  • Mayakan ISWAP sun rike manoma 76 daga sansanin ‘yan gudun hijira da ke Ngala a jihar Borno yayin da su ke gyara gonakin su su na cire bishiyoyi din shirin girbin shukokin su
  • Majiya daga tsagerun ta bayyana yadda mayakan su ka kwashe maza, mata da yara su ka wuce da su Chikongudo, wani gari da ke karkashin ikon mayakan ISWAP
  • Umar Kachalla, shugaban tsagerun, ya bayyana yadda ISWAP ta hana manoma sare shukoki a yankin don su zama kariya a gare su daga rundunar sojojin Najeriya

Borno - Mayakan kungiyar ta'addanci ta ISWAP sun rike wasu manoma 76 daga wani sansanin ‘yan gudun hijira a Ngala a ranar Juma’a na tsawon kwanaki biyu.

Jaridar The Guardian ta ruwaito yadda suka sace su yayin da su ke sare itatuwa da ciyayi don rage wa wurin duhu sakamakon yadda lokacin girbi ya ke karatowa.

Kara karanta wannan

Imo: Yadda mayakan IPOB suka kashe direbobin tirelar Dangote 3, suka babbaka gawawwakin su

Borno: ISWAP ta sako manoma 76 da ta kama, ta yi musu bulala kafin sakinsu
ISWAP ta sako manoma 76 da ta kamaa Borno, ta yi musu bulala kafin sakinsu. Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Mayakan ISWAP din sun kwashe maza, mata da kananun yara inda su ka wuce da su Chikongudo, wani gari da ke karkashin ikon su bisa ruwayar The Guardian.

Shugaban tsagerun, Umar Kachalla ya sanar da AFP cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“ISWAP ta ja kunnen manoman akan kone shukokin a yankin don gudun bude wa rundunar sojin Najeriya hanyar ganin mu cikin sauki.
“An sako su bayan an gama zane mazan, hakan zai zama horarwa da jan kunne a gare su.”

Har ila yau wani shugaban tsagerun, Umar Ari ya ce:

“Sun ci sa’a da ‘yan ISWAP ne su ka kama su ba ‘yan Boko Haram ba, da sun halaka maza sun mayar da mata da yara bayin su.”

ISWAP kishiyar Boko Haram ce a halin yanzu

ISWAP kungiyar adawar Boko Haram ce, kuma sun raba jiha ne tun 2016 saboda wani sabani da ya shiga tsakanin su akan yadda suke kai wa musulmai maza, mata da yara faramaki.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun mamaye gidan rasuwa, sun sace bakin da suka halarci jana’iza

Dukkan su sun ci gaba da kai wa masu sarar bishiyoyi don katako ko itace, manoma, makiyaya da sauran mutane farmaki bisa zargin su da kai wa sojoji da sauran masu yaki da su bayanai.

Sun dade suna kai wa makiyaya farmaki su na kwace shanun su don samun kudaden yin ta’addancin su.

Sun yi sanadin halaka fiye da mutane 40,000 sannan kusan mutane 2,000,000 ne su ka rasa gidajen su a yankin arewa maso gabas tun daga 2009.

Mafi yawan ‘yan gudun hijira sun dogara ne da abincin da a ke kai mu su taimako wasu kuma sun koma sarar bishiyoyi su na sayar da itace don su samu abinci.

A watan Disamban da ya gabata, mayakan Boko Haram su ka halaka manoman shinkafa 70 a gonar su da ke waje da babban birnin Maiduguri, bisa zargin su da hada kai da sojoji.

A watan Nuwamban 2018 ‘yan Boko Haram su ka halaka ma su yin katako 50 a kauyen Bulakesa kusa da Gamboru.

Kara karanta wannan

Mutane 200, 000 sun rungumi tsarin E-Naira a cikin awanni 24 da fitowa Najeriya

Rahoto: Masu ƙera wa Boko Haram bama-bamai sun koma dazukan Kudancin Kaduna

A baya, kun ji cewa shugabannin kungiyar Boko Haram da ke biyayya ga Bakoura Buduma sun mayar da masu hada musu bama-bamai dazukan yankin kudanci Kaduna, a cewar wani rahoton da PRNigeria ta fitar.

A baya-bayan nan ne aka mayar da masu hada bama-baman da ake kira Amaliyyah a tsakin 'yan ta'addan, zuwa Rijana, Igabi da Chikun a yankin kudancin Kaduna.

Majiyoyi daga ciki sun ce kungiyoyin biyu na Boko Haram za su yi amfani da duwatsun da ke yankin a matsayin mabuya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: