IGP Usman Baba: Babu makawa za a yi zaben gwamna a jihar Anambra
- ‘Yan sandan Najeriya sun bayyana jajircewar su akan ganin zaben jihar Anambra na gwamnoni da za a yi a ranar 6 ga watan Nuwamban 2021 ya tabbata
- Sifeta Janar na ‘yan Sanda, Usman Alkali Baba ya tabbatar wa da mazauna jihar ta kudu maso gabas cewa tabbas za ayi zaben kuma za su tabbatar da tsaro
- Mutane da dama na yankin a razane su ke saboda tsoron ‘yan kungiyar IPOB da su ka dade su na tilasta jama’a zaman gida don a sako shugaban su
Legas - Sifeta janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, ya lashi takobin ganin ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro sun tabbatar zaben gwamnoni mai gabatowa a jihar Anambra ya tabbata.
An samu bayanai akan yadda za a gudanar da zaben a jihar Anambra a ranar Asabar, 6 ga watan Nuwamba.
Yayin wani taro da mataimakin sifeta janar na ‘yan sanda, Zone 2, Onikan, jihar Legas, Johnson Babatunde Kokumo, IGP din ya ce za a yi zaben.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daily Sun ta ruwaito yadda IGP din ya bayar da tabbaci inda ya ce:
“Mun tanadi jami’an tsaro kashi 2 a jihar Anambra. Kashi daya za su kula da jama’a yayin zaben don tabbatar da cewa ba a cutar da kowa ba.
“Bangare na 2 kuma za su dinga duba ayyukan ta’addanci na kungiyoyi kamar IPOB, ESN da sauran su, don gudun su shiga hakkin jama’a.”
Shugaban INEC ma ya ce za a yi zaben
A bangaren shugaban hukumar zabe mai zaman kan ta ta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu ya tabbatar wa da mutanen jihar Anambra cewa tabbas za a yi zaben.
Ya kara da bayyana lokacin zaben inda ya ce za a yi ne a ranar 6 ga watan Nuwamba. Daily Trust ta yanko inda Farfesa Yakubu ya ke fadin hakan a Awka, ranar 2 ga watan Nuwamba.
A cewar sa zaben zai tabbata ne da taimakon jami’an tsaro wadanda za su jajirce wurin ganin an yi zaben gaskiya da gaskiya cikin tsaro.
Dan takarar gwamna ya sharɓi kuka a bainar jama'a yayin yaƙin neman zaɓe a Anambra
A wani rahoton, dan takarar gwamna na jam'iyyar Zenith Labour Party (ZLP) da za a yi a ranar 6 ga watan Nuwamba, Dr Obiora Okonkwo, ya zubar da hawaye a yayin da ya ziyarci garin Okpoko don kaddamar da aikin titi na miliyoyin naira a ranar Laraba.
Aikin titin zai fara ne daga Ede Road, School Road/Awalite da Ojo street ya tsaya a Owerri road a garin Okpoko a karamar hukumar Ogbaru a jihar ta Anambra, Daily Trust ta ruwaito.
Okonkwo ya zubar da hawaye ne a lokacin da ya ga wata mata mai shayarwa mai shekaru 30 wadda ta fada cikin kwata bayan ta kasa bin titin saboda rashin kyawunsa.
Asali: Legit.ng