Sabon Hari: Duk da dauke sabis, Yan bindiga sun sake kai wani mummunan hari a jihar Katsina
- Wasu tsagerun yan bindiga sun kai sabon hari yankin karamar hukumar Faskari dake jihar Katsina
- Mazauna yankin sun tabbatar da lamarin amma har zuwa yanzun ba'a san adadin yawan mutanen da suka mutu ba
- Wannan shine karo na biyu da yan bindiga suka kai hari yankin Faskari cikin kwanaki biyar kacal
Katsina - Premium Times ta rahoto cewa wasu tsagerun yan bindiga sun kashe adadin da ba'a sani ba na mutane a Unguwar Dudu, ƙaramar hukumar Faskari, a jihar Katsina.
Mazauna yankin sun tabbatar da faruwar lamarin, kuma maharan sun fasa shaguna suka ɗiba abinda suke bukata.
Wannan shine karo na biyu da yan bindiga suka kai hari Faskari cikin kwanaki 5, bayan wanda suka kai ƙauyen Unguwar Samanja.
Yadda lamarin ya faru
Habibu Mohammed, wani ɗan asalin yankin, amma yana zaune a Kaduna, yace an kashe masa kawunnai biyu yayin harin wanda ya kwashe minti 40.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya kuma bayyana sunayen yan uwansa da aka kashe da Alhaji Ado da Alhaji Bature, waɗan da yan kasuwa ne dake zaune a ƙauyen.
Muhammed yace:
"Lokacin da suka shiga ƙauyen, sun fara harbi kan mai uwa da wabi, kafin daga bisani su sauka daga abin hawa su fara ɗibar kayan shagunan mutane."
"Saboda rashin kawo ɗauki kasancewar babu sabis ɗin sadarwa, maharan sun ci karensu babu babbaka na tsawon mintuna 40, inda suka kashe mutane kuma suka jikkata wasu."
Mutum nawa maharan suka kashe?
Sai dai mutumin yace bai san adadin yawan mutanen da suka mutu sanadiyyar harin ba saboda yana zaune a Kaduna.
"Wani ɗan uwana ne yaje Gusau domin ya kira ni ta wayar salula ya sanar dani halin da ake ciki. Ban tambaye shi mutum nawa suka mutu ba, amma ya tabbatar mun da kawunnai na 2 sun mutu."
Hakazalika wani ɗan yankin, Babangida Gaikau, ya tabbatar da harin amma bai san adadin yawan mutanen da maharan suka kashe ba.
Kakakin yan sanda reshen jihar Katsina, Gambo Isa, bai ɗaga kiran wayar da aka masa ba, kuma bai dawo da amsar sakonni da aka tura masa ba.
Budurwa ta mutu bayan kwana dakin saurayi
A wani labarin kuma Wata Budurwa ta mutu jim kaɗan bayan ta kwana d dakin Saurayinta lokacin da ta kai masa ziyara
Rahoto ya nuna cewa ɗalibar mai suna Wumi, ta kamu da rashin lafiya ne jim kaɗan bayan dawowarta daga ɗakin, ta mutu akan hanyar zuwa Asibiti.
A halin yanzun yan sanda sun yi awon gaba da matashin saurayin domin gudanar da bincike.
Asali: Legit.ng