Shehu Sani: Kashe Sheƙau da Al-Barnawi ba zai kawo ƙarshen ta'addanci ba
- Shehu Sani, tsohon sanata mai wakilitar mazabar Kaduna ta tsakiya ya ce kisan shugabannin Boko Haram, Abubakar Shekau da Abu Musab Al-Barnawi ba zai kawo karshen rashin tsaro a arewa maso gabashin Najeriya ba
- Sani ya bayyana wannan ra’ayin na sa ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin a ranar Lahadi, inda ya ce kisan na su kawai zai kwantar da hankalin mutane ne
- Ya yi misali da kisan Osama Bin Laden inda ya ce bai kawo karshen Alqaeda ba da kuma kisan Al-Baghdadi a Iraq, inda ya ce duk wasu ‘yan ta’adda su na sabunta shugabanninsu bayan mutuwarsu
Kaduna -Tsohon sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya ce kisan shugabannin Boko Haram kamar Abubakar Shekau da Abu Musab Al-Barnawi ba zai kawo karshen ta’addanci a arewa maso gabas ba.
Bisa ruwayar Daily Trust, Sanatan ya bayyana wannan ra’ayin na sa ne yayin wata tattaunawa da Trust TV ta yi da shi a ranar Lahadi.
Ya kula da yadda mutuwar manyan ‘yan ta’addan ta kara wa sojoji kaimi sannan ya ce kungiyoyin ‘yan ta’addan su na ci gaba da wanzuwa duk da mutuwar shugabanninsu.
Kamar yadda ya bayyana:
“Kisan shugabannin ‘yan ta’adda abu ne mai kyau wanda zai sa sojoji su samu kwarin guiwa sannan ya ba mutane kwanciyar hankali. Sai dai idan ka kalli yadda lamarin ISIS ya auku, an halaka Al-Baghdadi a Iraq amma ISIS ta tafi? A’a. Kisan Osama bin Laden ya kawo karshen Alqaeda? Dole su ka sake dora wani shugaban.
“Ya na da kyau jami’an tsaro su san cewa don sun halaka shugaban ‘yan ta’adda , ba su kawo karshen ta’addanci ba.”
Ya misalta yadda Taliban ta dauki makami ta kwace shugabanci a Afghanistan
Ya kara da bayar da misali akan yadda Taliban su ka kara daukar makamai don yakar kasar su (Afghanistan) kuma su ka ci nasara.
A cewarsa, har yanzu ta’addanci yana nan kuma ‘yan ta’adda su na kara fadada ayyukan su a arewa maso gabas kamar yadda ya zo a ruwayar ta Daily Trust.
Dangane da batun tubabbun ‘yan Boko Haram, Sani ya ja kunne inda ya ce ya kamata sojoji su sa ido akan su saboda kada su yi wa jama’a kwanton bauna.
Sanatan ya bayyana cewa ya kamata a kula da su kafin su yi amfani da tubar da su ka yi wurin cutar da jama’a kuma a tabbatar su na da niyyar komawa rayuwa irin ta sauran mutane.
An kashe Dogo Giɗe, ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga da ya daɗe yana addabar jihohin arewa
A baya, Legit ta kawo muku wani rahoto da ya ce an kashe hatsabibin shugaban 'yan bindiga Dogo Gide.
An kashe shi ne a dajin Kuyanbana da ke jihar Kaduna kamar yadda PRNigeria ta wallafa.
A watan Maris na shekarar 2018, Gide ya kashe hatsabibin shugaban yan bindiga a wannan lokacin, Buharin Daji, bayan hakan ne ya zama shugaban yan bindigan yankin.
Asali: Legit.ng