An bankado yadda Buhari da Ministansa suka saba doka wajen bada kwangilar biliyoyi
- Gwamnatin tarayya ta sake dawo da tsarin International Cargo Tracking Note (ICTN) da aka soke a da.
- Ministan sufuri na kasa ya bada kwangilar wannan aiki ne ga kamfanin MedTech Scientific Limited.
- Bincike ya nuna an yi watsi da dokoki da ka’idojin aiki wajen bada wannan muhimmin kwangila.
Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari da Ministan sufuri, Rotimi Amaechi sun amince da wata kwangilar tsaro mai muhimmanci ga kamfanin kiwon lafiya.
Wani bincike da jaridar Premium Times ta gudanar, ya nuna cewa ma’aikatar BPP ta ji kunyar wannan kwangila da aka bada, tace an saba dokar gwamnati.
Wannan bincike ya jawo manyan jami’an gwamnatin tarayya na kokarin janye hannunsu daga wannan kwangila da ta ci karo da dokar bada kwangila na 2007.
International Cargo Tracking Note (ICTN)
A shekarun baya gwamnatin tarayya ta shigo da tsarin International Cargo Tracking Note (ICTN) domin binciken jiragen da suka shigo ko suka bar Najeriya.
A lokacin da Ngozi Okonjo-Iweala ta zama Ministar tattalin arziki, ta soke wannan tsari duk da kudin da ake samu, tace yana kawo tasgaro wajen kasuwanci.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A Agustan 2021 ne ma’aikatar sufuri ta yi kwadayin a dawo da wannan tsari. Tun a 2020, Rotimi Amaechi ya nemi izinin hukumar BPP domin dawo da shirin.
An saba ka'idar hukumar BPP
Hukumar BPP ba ta amince a ba kamfanoni gida wannan aiki ba, a dalilin yadda kwangilar da aka yi a baya ta kare a EFCC, ta bukaci a nemo kamfanin waje.
Abin mamaki sai aka ji labari a karshen Agustan 2021 cewa an samu sa hannun shugaban kasa wajen ba kamfanin MedTech Scientific Limited wannan aiki.
MedTech Scientific Ltd zai yi wannan kwangila ne tare da kamfanin Rozi International Nigeria Limited.
Binciken da jaridar ta yi, ya nuna cewa an ba MedTech Scientific Ltd wanda kamfanin kiwon lafiya ne wannan kwangila a boye, ba tare da an tallata aikin ba.
Babu abin da ke nuna kamfanonin nan sun taba yin wani aiki makamancin tsaron ruwa a Najeriya. Kuma ba a yi takara wajen neman kwangilar tsaron ba.
Da aka tuntubi hukumar BPP ta kasa, tace ba a tura mata sunayen wadanan kamfanoni biyu ba, don haka ba ta da masaniyar ko za su iya yin irin wannan aikin.
Wahalar man fetur
Rahotanni sun tabbatar da cewa dogayen layi sun fara bayyana a gidajen mai a garuruwan Abuja, Taraba, Kaduna da Nasarawa yayin da karshen shekara ya gabato.
A wasu garuruwan babu fetur a gidajen mai, ana cin kasuwar bumburutu. A Abuja, 'yan bumburutu na saida galan mai cin lita goma tsakanin N2500 da N3000.
Asali: Legit.ng