Labari da ɗuminsa: An kashe Dogo Giɗe, ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga da ya daɗe yana addabar jihohin arewa
- A karshe dai hatsabibin shugaban 'yan bindiga da ya dade yana addabar jihohin arewa, Dogo Gide ya bakunci barzahu
- Rahotanni sun bayyana cewa Sani Dan Makama, mataimakin Dogo Gide ne ya bindige shi har lahira a ranar Lahadi a dajin Kuyambana
- Wani karamin rikici ne ya shiga tsakanin Gide da Dan Makama har ta kai ga ya bindige shi, hakan ya yi kama da yadda Gide ya kashe Buharin Daji
Rahoton da muka samu daga PRNigeria ya ce an kashe hatsabibin shugaban 'yan bindiga Dogo Gide.
An kashe shi ne a dajin Kuyanbana da ke jihar Kaduna.
A watan Maris na shekarar 2018, Gide ya kashe hatsabibin shugaban yan bindiga a wannan lokacin, Buharin Daji, bayan hakan ne ya zama shugaban yan bindigan yankin.
Wata majiya ta shaidawa PRNigeria cewa Gide ya mutu ne a ranar Lahadi bayan mataimakin kungiyarsa na yan bndiga, wani Sani Dan Makama ya bindige shi kamar yadda ya yi wa Buharin Daji.
Tsohon shugaban 'yan bindigan ya dade yana adabar garuruwa a jihohin Zamfara, Niger, Kaduna, Katsina da Kebbi tsawon shekaru.
Majiyar ta ce:
"Mataimakin Dogo Gide wanda ake kira Sani Dan Makama ne ya kashe shi bayan wani sabani da ya shiga tsakaninsu a dajin Kuyambana da ya hada Zamfara - Birnin Gwari da Dogon Dawa."
Dogo Giɗe, hatsabibi shugaban ƴan bindiga ya haramta shan giya da kayan maye a wasu ƙauyukan Zamfara
A baya, kun ji cewa Dogo Gide, hatsabibin dan bindiga, ya saka dokar hana siye da siyar da giya da sauran muggan kwayoyi a wasu garuruwan masarautan Dansadau da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.
Shugaban 'yan bindigan da ke zaune a dajin Kuyambana, da ya ratsa ta jihohin Zamfara, Kaduna, Niger da Kebbi ya kwace iko a garin Babbar Doka, Daily Trust ta ruwaito.
Ya gargadi mazauna kauyukan cewa a bainar jama'a za a kashe duk wanda aka kama yana sayar da miyagun kwayoyi ko kuma shan su.
Saurari karin bayani ...
Asali: Legit.ng