Shugaba Buhari ya tafi Birtaniya, daga nan kuma zai tafi Faransa
- Jirgin Shugaban kasa ya shiga sararin samaniya inda ya nufa shiga kasar Birtaniyya nan da wayewar gari
- Wannan na faruwa ne kwana biyu kacal bayan dawowarsa daga kasar Saudiyya inda ya gudanar da ibadar Umrah
- Shugaban kasan ya samu rakiyar Ministoci biyu da kuma manyan shugabannin hukumomin tsaro biyu
Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi birnin Glasgow, Scotland don halartan taron COP26 na taron gangamin majalisar dinkin duniya kan sauyin yanayi.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Lahadi, 31 ga Oktoba, 2021.
Kana ya bayyana cewa Buhari zai gabatar da jawabi a taron ga shugabannin kasashen duniya ranar Talata, 2 ga Nuwamba, 2021.
Jirgin Buhari ya tashi daga tashar jirgin Nnamdi Azikwe dake birnin tarayya Abuja gaban Magariba.
Buhari ya samu rakiyar Ministan wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama; Karamar ministar yanayi, Sharon Ikeazor; NSA Babagano Munguno; DG NIA, Amb. Ahmed Rufai Abubakar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daga nan kuma zai garzaya Faransa
Garba Shehu ya bayyana cewa bayan taron sauyin yanayi a Birtaniya, Shugaba Buhari zai tafi kasar Faransa domin halartan taron zaman lafiya a Paris.
Yace:
"Shugaba Buhari daga baya zai tafi Paris, Faransa domin ziyara ga Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, domin nuna godiya bisa ziyarar da Shugaban kasan Faransan ya kawo Najeriya a baya."
Yaushe zai dawo?
Mai magana da yawun Buhari bai bayyana lokacin da Shugaban kasan zai dawo ba idan ya tafi yau.
Legit Hausa ta yi yunkurin tuntubar fadar shugaban kasa domin sanin yaushe zai dawo amma abin ya ci tura.
Shugaba Buhari Ya dawo daga Kasar Saudiyya
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya dira a birnin tarayya Abuja da yammacin Juma'a, 29 ga Oktoba, bayan tafiyar kwana biyar da yayi Kasar Saudiyya.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ta ruwaito cewa Shugaba Buhari da mukarrabansa sun tashi daga filin jirgin Sarki AbdulAzizi dake Jiddah misalin karfe 15:45.
Asali: Legit.ng