Mun kammala bincike a kan Abba Kyari - Shugaban ‘Yan Sanda ya fadi abin da ake jira
- Usman Alkali Baba yace bai samu wata takarda a ofishinsa da ta ke rokon a damka DCP Abba Kyari domin bincike ba
- Sufetan ‘Yan Sandan na kasa yace a kafafen sadarwa ya ji wannan labari, ya kuma fadi kokarin da suke yi a kai
- IGP ya bayyana cewa kwamitin da ya kafa ya kammala bincikensa tuni, kuma ya gabatar da rahoto a kan teburin SGF
Abuja - Shugaban ‘yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya yi magana game da rade-radin cewa Amurka ta bukaci a mika mata Abba Kyari.
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Alhamis, 28 ga watan Oktoba, 2021, inda aka ji Usman Alkali Baba yana cewa bai san da maganar nan ba.
IGP Alkali Baba yace sam bai da labarin hukumomin kasar Amurka sun gabatar da takarda, suna neman a mika masu jami’in ‘dan sandan Najeriyar.
Hakan na zuwa ne bayan an yi ta jita-jita cewa hukumar FBI mai bincike a Amurka ta nemi a damka mata DCP Abba Kyari da nufin a bincike shi.
Da yake magana da manema labarai a fadar shugaban kasa, gidan talabijin na Channels TV ya rahoto sufetan ‘yan sandan yana musanya rade-radin.
Rahoton yace Sufeta Janar na ‘yan sandan ya bayyana wannan da yake magana a birnin Abuja.
Ban san da wannan magana ba - IGP
Shugaban ‘yan sandan yace bai da labarin wata takarda da aka aiko kan wannan bukata, illa abin da yake karantawa a shafukan sada zumunta na zamani.
IGP Baba yace ya samu takarda daga ofishin babban lauyan da ke kare gwamnati, Abubakar Malami SAN, a kan shawarar abin da ya kamata ya yi.
Baba yace suna aiki a kan wannan takarda, kuma za su nemi jin ta bakin jami’in domin ya bada amsoshi kan abin da suka gano daga binciken da aka yi.
IGP yace da labarin ya taso, an kafa kwamiti da ya yi bincike a kan jami’in da ake zargi, kuma an gabatar da rahoton gaban teburin SGF, yana neman shawara.
Abba Kyari ya shiga matsala
Kwanakin baya aka ji hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta dakatar da Abba Kyari bisa zargin cin hanci.
Ana zargin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari da hannu a badakalar Hushpuppi wanda yanzu haka yake tsare a hannun jami’an na Amurka.
Asali: Legit.ng