Yanzu-yanzu: 'Yan ta'adda da motocci masu bindiga 15 suna can sun kai hari Damboa
- 'Yan ta'adda da ake kyautata zaton 'yan kungiyar ISWAP ne suna can sun kai gari garin Damboa da ke jihar Borno, arewa maso gabashin Nigeria
- Wasu mutanen garin da suka tabbatar da harin sun ce 'yan ta'addan sun shigo tarin da motocci 15 masu bindigu suna ta harbe-harbe
- Wata majiya daga jami'an tsaro ta ce dakarun sojoji suna can sun tari 'yan ta'addan suna kokarin fatattar su amma suna son taimakon sojojin sama
Jihar Borno - Wasu 'yan ta'adda da ake zargin yan kungiyar Islamic State in West Africa Province (ISWAP) ne suna can sun kai hari garin Damboa a jihar Borno.
Damboa yana nan kimanin kilomita 90 ne daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa yan ta'addan sun shigo ne ta hanyar Biu-Damboa misalin karfe 7 na yammacin ranar Alhamis.
Majiyoyi daga garin, wadanda suka yi magana da The Cable daga inda suka boye, sun kirga motocci masu bindiga 15 lokacin da yan ta'addan suka kutsa garin.
Majiyar ta ce:
"Mutane na harkokin su da suka saba ne a yayin da muka fara jin karar harbin bindiga a yammacin yau.
"Tunda farko mun yi zargin suna tahowa kusa da Sabon Gari a hanyar Biu-Damboa kafin sun iso nan. A yanzu ba za mu iya sanin ko an rasa rai ba tunda har yanzu suna cikin garin.
"Yan ta'addan sunyi karfi a kusa da hanyar Biu-Damboa. Wasu lokutan ma suna saka shige a kan hanya."
Sojoji suna can suna fafatawa da 'yan ta'addan
The Cable ta gano cewa dakarun sojojin Nigeria na 25 task force brigade a Damboa tuni sun tunkari yan ta'addan.
Harin na Damboa na zuwa ne kwana guda bayan harin da aka kai garin Kwada da ke karamar hukumar Chibok da ke makwabtaka da karamar hukumar Damboa.
Mazauna garin da suka yi magana da majiyar Legit.ng sun ce yan ta'addan sun fara kaiwa sojojin da ke garin hari kafin suka karaso kan mutanen gari.
An tura sojojin ne daga 117 task force brigade da ke Chibok.
Ba a samu ji ta bakin mai magana da yawun rundunar sojoji ba, Onyema Nwachukwu domin jin abin da zai ce game da harin.
Sai dai, wani jami'n tsaro a yankin ya shaidawa The Cable cewa sojojin na iya kokarinsu domin fatattakar yan bindigan amma za su bukaci taimakon sojojin sama.
Ya ce:
"Muna kira a turo mana jiragen yaki domin hakan zai taimaka mana fatattakar su."
Asali: Legit.ng