Yan sanda sun damke wani mutumi kan laifin turawa matar aure sakon "Inakwana Baby na"

Yan sanda sun damke wani mutumi kan laifin turawa matar aure sakon "Inakwana Baby na"

  • Wani mutumi ya shiga komar yan sanda bayan turawa matar aure sakon da ka iya sama mata matsala a gidan aure
  • Jami'an yan sanda sun damke matashin mai shekaru 38 inda suka tuhumcesa da laifin kokarin tada tarzoma
  • Yan Najeriya a Soshiyal Midiya sun tofa albarkatun bakinsu kan wannan takaddama dake faruwa

Wani dan Najeriya mai suna Sikiru Oluwaseun Jamiu ya shiga hannun jami'an yan sanda kan laifin turawa matar aure mai suna Opeyemi Adegbesan sakon "Ina Kwana Baby".

Hukumar ta bayyana cewa ya tura wannan sakon ne ranar 19 ga Satumba, 2021.

Shin Wannan laifi ne?

A hoton da @instablog9ja ta wallafa, Sikiru ya tura sakon nan ta manhajar WhatsApp kuma hakan ya sabawa sashe 249 (d) na dokokin jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Yadda yan majalisun PDP da APC suka fafata wajen tsige shugaban majalisar dokokin Filato

A cewarsu, abinda Sikiru yayi na iya zama matsala ga auren Opeyemi da mijinta Akintunde.

An damke mutumin kan laifin turawa matar aure sakon "Inakwana Baby na"
Yan sanda sun damke mutumin kan laifin turawa matar aure sakon "Inakwana Baby na" Photo credit: @instablog9ja
Asali: Instagram

Budurwata rabuwa da ni tayi lokacin da rasa aikina a Banki, Matashin da ya koma aikin direba

A wani labarin kuwa, wani matashin direba ya bayyana mugun halin da ya shiga na rashin kudi da kuma rashin budurwarsa lokacin da ya rasa aikinsa a bankin Beige a Ghana.

A Agustan 2018, Bankin Ghana (BoG) ta janye lasisin Beige Bank da wasu bankunan kasar hudu.

Sauran bakunan sune uniBank Ghana Limited, Royal Bank Limited, Sovereign Bank Limited da Construction Bank Limited.

Matashin yanzu ya koma aikin direba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng