An yi babban rashi: Allah ya yiwa mai masallacin matafiya da ke hanyar Kaduna-Zariya rasuwa
- Allah ya yiwa mai sanannen masallacin nan na matafiya da ke a hanyar babban titin Kaduna zuwa Zariya, Alhaji Sule Bako, rasuwa
- Bako ya rasu ne a wani asibiti mai zaman kansa da ke Abuja a ranar Laraba, 27 ga watan Oktoba
- An kuma yi jana'izarsa a jihar Kaduna inda ya yi jama'a sosai saboda ayyukansa na jin kan marasa gata
Jihar Kaduna - Mai sanannen masallacin nan na matafiya da ke a hanyar babban titin Kaduna zuwa Zariya, Alhaji Sule Bako, ya rasu.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mai aikin jin kan ya rasu ne a wani asibiti mai zaman kansa da ke babbar birnin tarayya Abuja, a ranar Laraba, 27 ga watan Oktoba.
An kuma yi jana'izarsa da misalin karfe 1:00 na rana a jihar Kaduna. Ya rasu yana da shekaru 84 a duniya.
Jaridar ta kuma rahoto cewa marigayin ya samu jama'a sosai, domin a lokacin da wakilinta ya ziyarci gidansa da ke hanyar Wushishi Road, Kaduna, ya gano dandazon jama'a da suka hallara domin taya iyalinsa alhinin wannan rashi.
Daya daga cikin yaransa mai suna Yusuf Sule Bako, ya bayyana marigayin a matsayin uba nagari wanda ke da riko da addini sosai.
Ya ce:
"Ya kasance uba nagari wanda ya kare rayuwarsa wajen yi wa addinin Musulunci da marasa gata hidima. Mun taso mun ga yana taimakon talakawa da kuma kula da masallatai."
Hakazalika, wani dan uwan marigayi Bako ya fada ma Daily Trust cewa da wuya a samu wanda zai maye gurbinsa.
Ya kuma bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi ga iyalan, jihar Kaduna da ma Najeriya, inda ya kara da cewa marigayin ya kasance jagora abun koyi wanda ake wa lakabi da Mai Gaskiya lokacin da ya yi ciyaman na kwamitin rikon kwarya a karamar hukumar Kaduna.
An binne shi daidai da koyarwar addinin Islama. Ya kuma rasu ya bar yara 13 da jikoki.
Allah ya yiwa Dan Makwayon Kano, Alhaji Sarki Aminu Bayero, rasuwa
A wani labarin kuma, mun kawo a baya cewa Allah yayiwa Alh. Sarki Aminu Bayero mai saurautar Dan Makwayon Kano rasuwa da daren Talata, 27 ga watan Oktoba, 2021.
Legit ta tattaro daga Jikokinsa akalla biyu wanda suka tabbatar da rasuwar marigayin.
Aminu Ali Muhd a shafinsa na Facebook, ya bayyana mutuwar kakansa kuma ya bukaci al'umma su roka masa Aljannah.
Asali: Legit.ng