Kotu ta ɗaure wani matashi da ya yi asubanci ya tafi coci ya sace kujerun roba

Kotu ta ɗaure wani matashi da ya yi asubanci ya tafi coci ya sace kujerun roba

  • Wata kotun majistare ta yanke wa wani matashi mai shekaru 19 daurin watanni 3 bisa tafka sata
  • Matashin ya saci kujerun wata coci ne masu kimar N91,200 a ranar 23 ga watan Oktoba
  • Kamar yadda rahoto ya bayyana, ya yi asubanci zuwa cocin ne don yin sata, ‘yan sa kai su ka kama shi

Ogun - A ranar Laraba wata kotun majistare ta daure wani matashi, Lekan Alaka, mai shekaru 19, watanni 3 bisa satar kujerun roba masu kimar N91,200 daga cocin Mount Zion Angelican.

‘Yan sandan sun kama Alaka da laifin sata kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kotu ta ɗaure wani mai matashi da ya saci kujerun roba a coci
Kotu ta ɗaure wani mai matashi da ya saci kujerun roba a coci. Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan Hisbah sun kama Aliyu Na Idris da ke son sayar da kansa kan N20m domin talauci

Alkali Olajumoke Somefun ya yanke hukunci bisa tabbatar da laifin da ya aikata bisa ruwayar Vanguard.

Somefun ya yanke wa Alaka watanni 3 a gidan yari ko kuma ya bayar da tarar N100,000.

Da farko dai mai gabatar da kara, ASP Olakunle Shonibare ya sanar da kotu cewa mai laifin ya aikata laifin da misalin karfe 4:30am na ranar 23 ga watan Oktoba a cocin Mount Zion Angelican, wuraren Leme a Abeokuta.

Shonibare ya ce mai laifin ya dira ta katanga sannan ya sace kujeru 24 masu tsadar N91,200 a cocin Mount Zion Angelican.

Ya ce ‘yan sa kai ne su ka kama shi yayin da yake yunkurin tserewa da kujerun da ya sace.

A cewar sa laifin ya ci karo da sashi na 415 na manyan laifukan jihar Ogun na 2006.

An yanke wa Salisu ɗaurin gidan yari kan satar tukwane da kujeru a coci a Legas

Kara karanta wannan

Matashin da ya yi wuf da wayoyin karuwai 2 bayan ya kai su otal yin lalata, an damkeshi

A wani rahoton mai kama da wannan, Alkali a kotun majistare da ke zamanta a Surelere, Legas a ranar Juma'a ya yanke wa wani Ibrahim Salisu hukuncin daurin watanni shida saboda satar kayayyakin da kudinsu ya kai N300,000 daga cocin Deeper Life da ke kallon Aina Street, Surulere.

A cewar dan sanda mai shigar da kara, Sufeta Courage Ekhueorohan, wanda ake zargin, Salisu ya aikata laifin ne a ranar 2 ga watan Yuni, ruwaiyar NewsWireNGR.

Ya ce Salisu ya kutsa cikin cocin ya sace manyan tukwane biyu na aluminium, tukwanen soye-soye, kujerun roba biyar, kwanuka biyu da wasu karafa na mimbari da kudinsu ya kai N300,000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164