Matashi ya tura sakon zagi ga hadimin gwamnan Katsina, ya gamu da fushin 'yan sanda

Matashi ya tura sakon zagi ga hadimin gwamnan Katsina, ya gamu da fushin 'yan sanda

  • 'Yan sanda a jihar Katsina sun kama wani matashi dan shekaru 39 mai suna Ahmed Abdulmumini
  • An kama Abdulmumini bayan ya tura sakon zagi ga hadimin gwamnan jihar, Alhaji Ibrahim Umar a ranar bikin zagayowar ranar haihuwarsa
  • Hadimin gwamnan ne ya shigar da kara ofishin 'yan sanda inda aka gano cewa sakon ya fito ne daga Abdulmumini wanda tuni ya amsa laifinsa

Jihar Katsina - Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta damke wani matashi dan shekaru 39 mai suna Ahmed Abdulmumini, kan zargin cin zarafi ta yanar gizo.

A cewar 'yan sandan, an kama Abdulmumini ne bayan wani korafi da hadimin Gwamna Aminu Bello Masari kan harkokin cikin gida, Alhaji Ibrahim Umar ya shigar.

Matashi ya tura sakon zagi ga hadimin gwamnan Katsina, ya gamu da fushin 'yan sanda
Matashi ya tura sakon zagi ga hadimin gwamnan Katsina, ya gamu da fushin 'yan sanda Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Umar ya sanar da 'yan sandan cewa wanda ake zargin ya yi kalaman batanci a kan shi ta sakon email, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: IGP ya tura manyan 'yan sanda sama da 100 kan barazanar IPOB

Ya yi ikirarin cewa ya ga sakon zagin ne yayin da yake bibiyar sakonnin fatan alkhairi daban-daban da mutane suka aike masa a ranar bikicin cikarsa shekaru 55 a duniya a ranar 25 ga watan Oktoba, 2021.

Kakakin 'yan sandan jihar, SP Gambo Isah, wanda ya tabbatar da lamarin a ranar Talata, 26 ga watan Oktoba, ya ce 'yan sandan sun gano nasabar sakon email din da Abdulmumini.

Ya ce:

"Don haka an kama Abdulmumini; kuma ya amsa laifinsa a lokacin da ake masa tambayoyi cewa ya aiko da sakon email din. Ya aikata wani laifi a karkashin sashe na 24 (1) A & B na dokar aikata laifuka ta Intanet, 2015."

Wanda ake zargin bayan gurfanar da shi a hedkwatar rundunar da ke Katsina a ranar Talata, ya ce bai yi nufin zagin hadimin gwamnan ba a sakon.

Kara karanta wannan

Tsananin kishi ya sa saurayi ture budurwarsa har lahira a Bauchi

Rahoton ya nakalto shi yana cewa:

"Da gaske na aika masa sakon email, amma ba nufin na yi masa ba'a ko bata masa suna ba."

An kama wani matashi bayan ya yi barazanar sace Shugaban al’umman Hausawa a Benin

A wani labarin kuma, jami’an ‘yan sandan jihar Edo sun kama wani mazaunin Kano mai shekaru 21, Yakubu Idris.

An kama Idris ne bisa zargin cewa yana barazanar yin garkuwa da shugaban Hausawa a garin Benin, Alhaji Badamasi Saleh, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Wanda ake zargin ya shiga hannu ne bayan korafi da Alhaji Badamasi Saleh ya shigar kan cewa wani mutum da bai san ko wanene ba yana barazanar sace shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng