Gwamnatin Buhari ta amince da biyan kudin kammala titin Gombe zuwa Biu

Gwamnatin Buhari ta amince da biyan kudin kammala titin Gombe zuwa Biu

  • Gwamnatin tarayya ta amince ta cire isassun kudi domin kammala ayyukan tituna da yawa a kasar nan
  • Gwamnatin ta ce, cikin titunan har da na Gombe zuwa Biu, wanda ya jima yana bukatar aikin gyara
  • Najeriya na da tituna da yawa da ke bukatar gyara, lamarin da ke kara jawo cece-kuce a kasar

Abuja - A ranar Talata ne gwamnatin tarayya ta ce za a samar da isassun kudade domin kammala dukkan manyan titunan gwamnatin tarayya a fadin kasar nan kan lokaci, ciki har da titin Gombe zuwa Biu.

Babban sakataren ma’aikatar ayyuka da gidaje Hassan Musa ne ya bada wannan tabbacin a Abuja yayin da yake jawabi ga shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar, Muktar Betara.

Kara karanta wannan

Take hakkin dan Adam: UN ta aiko wa Najeriya wasika, ta bukaci bayanai 5 game da kamen Kanu

Muktar Betara ya samu rakiyar Hon Ahmadu Usman Jaha da Kabir Tukura a ziyarar aiki da suka kai ma’aikatar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin Buhari ta amince da biyan kudin gyara hanyar Gombe zuwa Biu
Aikin titi a wani yankin Najeriya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ya ce ma’aikatar ta samu sabbin kudade na aikin hanyar Gombe zuwa Biu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu yankuna daban-daban a Najeriya na fama da matsalar fashewar hanyoyi, lamarin ya jawo munanan hadurra a kan hanyoyin.

Direbobin tanka da tirela a jihar Neja sun gudanar da zanga-zanga kan rufe hanyar Minna zuwa Bida da gwamnatin jihar ta yi, inda gwamnati ta zargi manyan motocin da lalata hanyoyi, This Day ta ruwaito.

Hotunan mumunan hadarin mota da ya auku tsakanin Tirela motoci 11 daren Juma'a a Abuja

A wani labarin, Hukumar kiyaye lafiyan hanya ta Najeriya, FRSC, ta tabbatar da labarin mumunan hadarin da ya shafi motoci 11 da ya faru daren Juma'a, a babban titin Kubwa dake birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga: Sarkin Birnin Gwari ya bayyana alherin da katse hanyoyin sadarwa ya jawo

BBC Pidgin ta ruwaito cewa Kakakin hukumar FRSC, Bisi Kazeem, ya tabbatar da hakan.

A cewarsa, Tirela guda ne da motoci 11 suka ci karo da juna kuma mutum daya ya mutu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.