Bayan kwanaki 4 da balle gidan, 'Yan sanda sun cire bam a gidan gyaran halin Oyo
- Bayan kwana hudu da balle gidan gyaran hali na Abolongo da ke Oyo, an gano bam a wajen gidan
- Sai dai mai magana da yawun hukumar gidan, Olarewanju Anjorin, ya ce 'yan sanda sun cire
- Jami'an da ke kula da gidajen gyaran halin jihar ne suka ga bam din wanda 'yan ta'adda suka dasa
Abolongo, Oyo - Kwanaki hudu bayan 'yan bindiga sun kai farmaki tare da sakin daruruwan jama'a daga gidan gyaran hali da ke Abolongo a jihar Oyo, 'yan sanda sun cire bam a gidan.
Wata majiya ta sanar da Daily Trust cewa, bam din ya na daga cikin wadanda 'yan ta'adda suka dasa yayin farmakin da suka kai gida a ranar Juma'a da ta gabata.
Yayin da aka tuntubi mai magana da yawun hukumar gidajen gyaran hali ta jihar, Olanrewaju Anjorin, ya tabbatar da aukuwar lamarin, The Guardian ta wallafa.
"Da gaske ne amma 'yan sanda sun cire bam din bayan wasu daga cikin ma'aikatan gidan gyaran halin sun gano cewa an dasa abu mai fashewa ta wajen gidan," yace.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An tattaro cewa, 'yan sanda sun cire abun mai fashewa a wajen gidan gyaran halin wurin karfe 2 na rana kuma babu wanda ya rasa ransa ko ya ji rauni.
Yan bindiga sun fasa gidan yari a jihar Oyo, Sun saki fursunoni duka
A wani labari na daban, jaridar Vanguard ta rahoto cewa wasu tsagerun yan bindiga sun kai hari gidan yarin dake Abolongo, a jihar Oyo ranar Jumu'a da daddare.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kutsa cikin gidan yarin, sannan suka saki dukkan fursunonin dake ciki.
Miyagun yan bindigan sun fasa gidan yari ne da tsakar dare, inda suka yi amfani da gurneti wajen tilasta samun damar shiga harabar gidan gyaran halin.
Harin ya jefa gidan gyaran halin cikin mawuyacin hali, yayin da masu gadin wurin suka watse domin neman hanyar tseratar da rayuwarsu.
Kakakin hukumar tsaron gidan gyaran hali (NCS) reshen jihar Oyo, Olanrewaju Anjorin, ya tabbatar da kai harin.
Dailytrust ta ruwaito kakakin yace: "Mun tabbatar da cewa an kai hari, kuma a halin yanzu shugaban NCS na jiha da sauran manyan jami'ai suna nazari kan matakin da za'a ɗauka."
Asali: Legit.ng