CAN ga FG: Ya kamata a garkame Sheikh Gumi saboda yiyuwar alaka da 'yan bindiga

CAN ga FG: Ya kamata a garkame Sheikh Gumi saboda yiyuwar alaka da 'yan bindiga

  • Kungiyar CAN ta nemi gwamnatin tarayya da ta gaggauta kama shahararren malamin nan na addinin Musulunci, Sheikh Ahmed Gumi
  • CAN ta kuma bukaci hukumomin tsaro da su binciki ikirarin Gumi na cewa ayyana 'yan fashin daji a matsayin 'yan ta'adda zai zo da tarin nadama
  • Ta ce gwamnati na yi wa lamarin Gumi rikon sakainar kashi alhanin Najeriya ba tashi bace

Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) a ranar Talata, 26 ga watan Oktoba, ta kalubalanci gwamnatin tarayya da ta yi gaggawan kama shahararren malamin nan na addinin Musulunci, Sheikh Ahmed Gumi.

Kungiyar ta kuma nemi hukumomin tsaro da su dauki mataki ta hanyar binciken ikirarin da malamin yayi na cewa ayyana ‘yan fashin daji a matsayin ‘yan ta’adda zai zo da tarin nadama, Vanguard ta ruwaito.

CAN ga FG: Ya kamata a garkame Sheikh Gumi saboda yiyuwar alaka da 'yan bindiga
CAN ga FG: Ya kamata a garkame Sheikh Gumi saboda yiyuwar alaka da 'yan bindiga Hoto: The Nation
Asali: UGC

Idan za ku tuna, Gumi, cikin sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, ya ce akwai abubuwa masu hatsari da ka iya biyo bayan ayyana ‘yan fashin daji a matsayin ‘yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta lashi takobin tsamo ‘yan Najeriya miliyan 2 daga jahilci duk shekara

Da yake martani kan haka, daraktan lamuran da suka shafi jin dadin zamantakewa na CAN, Bishop Stephen Adegbite, ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Gwamnatin tarayya na yi wa lamarin Sheikh Ahmed Gumi rikon sakainar kashi.
"Abin takaici ne kuma mun damu, muna cike da takaici da jin zafi cewa zai yi irin wannan magana kai tsaye ba tare da an kalubalance shi ba.
“Amma Cocin ba zai kara yin shiru ba. Ya isa haka. Daga yanzu za mu dauke shi kalma bayan kalma.
“Ya kamata gwamnatin tarayya tayi abun da ya dace sannan ta kama shi. Shin Gumi ne ke da Najeriya?
“Me ya taka da zai kalubalanci hukuncin mutane cewa ‘yan bindiga makiya ne da ke neman tarwatsa kasarmu?
“Ya zama dole wani ya taka masa birki. Ya zama dole ya daina yi wa ‘yan Najeriya da Najeriya barazana. Ya kamata Gumi ya kasance a kurkuku."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga: Sarkin Birnin Gwari ya bayyana alherin da katse hanyoyin sadarwa ya jawo

Sheikh Gumi: Za a yi nadamar ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda

A baya mun kawo cewa Shiekh Ahmad Gumi, fitaccen malamin addinin musulunci ya ce masu ikirarin yin jihadi daga kasashen waje na iya shigowa Nigeria idan aka ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda.

Tun da baya, malamin ya taba rokon gwamnatin tarayya ta yi wa 'yan bindigan afuwa sannan ta basu tallafi don sauya halayensu su kama sana'a.

Da ya ke tsokaci kan kiraye-kirayen da ake yi a baya-bayan nan na neman a ayyana 'yan bindiga a matsayin yan ta'adda, Gumi, cikin sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, akwai abubuwa masu hatsari da ka iya biyo baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng