Matashin da ya yi wuf da wayoyin karuwai 2 bayan ya kai su otal yin lalata, an damkeshi

Matashin da ya yi wuf da wayoyin karuwai 2 bayan ya kai su otal yin lalata, an damkeshi

  • Kotu ta yanke wa Ejiro Tega watanni 14 a gidan gyaran tarbiyya na Kirikiri a Legas
  • Hakan ya biyo bayan satar da ya yi wa karuwai 2 na wayoyin su ma su tsada
  • Dama ya dauke su ne zuwa Otal da suna zai yi lalata da su, daga nan ya yi awon gaba da wayoyin

Legas - A ranar Talata, Alkalin wata kotun majistare da ke zama a Ikeja ya yanke wa Ejiro Tega watanni 14 a gidan gyaran hali na Kirikiri bisa ruwayar The Nation.

Alkali Elizabeth Adeola ce ta yanke hukuncin bayan Tega ya amsa laifuka 2 da ake zargin sa da su, na sata da karantsaye ga kwanciyar hankalin jama’a.

Kotu ta ɗaure matashin da ya yi wuf da wayoyin karuwai 2 bayan ya kai su otal don suyi lalata
Kotun Kostamare na Jihar Legas. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

The Nation ta rahoto cewa Kotu ta yanke masa watanni 14 ne sannan ba ta ba shi damar biyan tara ba, hasali ma cewa ta yi wajibi ne ya yi watannin tare da ayyuka masu tsananin gaske.

Kara karanta wannan

Ba zan iya zama da matata ba, tamkar a wuta nake: Magidanci ya roki 'yan sanda su kai shi gidan yari

Dama mai gabatar da kara, Sifeta Kenrich Nomayo, ya ce Tega ya kai karuwan, Blessing Joseph da Victoria Joseph zuwa otal ne, daga nan ya sace mu su wayoyin su.

A cewar sa, Tega ya sace waya kirar Tecno POP mai kimanin tsadar N63,000 da kuma wata Infinix Hot 10 mai tsadar N85,000 daga matan.

Yadda lamarin ya faru

Nomayo ya shaida wa kotu cewa Tega ya aikata laifukan a ranar 7 ga watan Satumba a Otal din Humble Heritage a Mafoluku dake Oshodi jihar Legas.

Ya ce mai laifin ya yaudari matan da sunan zai yi lalata da su a otal din, daga nan ya yi awon gaba da wayoyin su.

Kamar yadda ya ce:

“Mai laifin ya dauki matan da sunan zai shakata tare da su a otal.

Kara karanta wannan

Na sayar da diyata N150,000 ne don in biya kudin haya, Mahaifiya

“Har daki ya tanadar mu su a otal din daga nan ya nemi su shiga bayi su yi wanka.
“Ya koma dakin cikin hanzari sannan ya sace wayoyin su.”

Ya kara da cewa Tega ya yi karan tsaye ga zaman lafiya.

NAN ta ruwaito cewa laifukan da ya aikata sun saba wa sashi na 168 da 287 na dokar laifuka na jihar Legas ta 2015.

An sha mamaki bayan gano cewa gardin namiji aka tura gidan yari na mata ba tare da an gane a kotu ba

A wani rahoton, wani lamari mai ban mamaki ya auku a gidan gyaran halin mata da ke Shurugwu a makon da ya gabata, inda aka gano wata fursuna ba mace bace, katon namiji ne kamar yadda LIB ta ruwaito.

Praise Mpofu mai shekaru 22 ya na sanye da suturar mata ne a lokacin da aka kama shi inda ya bayyana kamar karuwa don ya yaudari maza ya yi musu sata.

Kara karanta wannan

Bayan ƙwace motarsa da IPhone, Alƙali ya umarci ɗan 'Yahoo-Yahoo' ya yi sharar harabar kotu na watanni 6

An kama Mpofu ne bayan ya yi wa wani mutum da ke yankin Gweru sata. An samu rahoto akan yadda mutumin ya caskewa Mpofu kudi don su kwana tare da shi a tunanin sa mace ne, daga nan Mpofu ya yashe shi ya tsere.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164