Fusatattun jam'an gari sun sheƙe wani ɗan leken asirin yan bindiga da iyalansa a Kaduna

Fusatattun jam'an gari sun sheƙe wani ɗan leken asirin yan bindiga da iyalansa a Kaduna

  • Wasu fusatattun mutane sun hallaka wani da ake zargin ɗan leken asiri ne tare da matarsa da kuma ɗansa a jihar Kaduna
  • Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, yace gwamnatin Kaduna ta yi Allah wadai da irin wannan aikin
  • Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa', ya yi kira ga mutane su daina ɗaukar doka a hannunsu

Kaduna - Wasu fusatattun jama'an gari sun hallaka wani da ake zargin mai baiwa yan bindiga bayanai ne da iyalansa a ƙaramar hukumar Igabi jihar Kaduna.

Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a dandalin Facebook.

A cewarsa hukumomin tsaro sun tabbatar da mutane sun kashe mutumin, matarsa da kuma ɗansu guda ɗaya a kauyen Zangon Aya dake Igabi.

Kara karanta wannan

An kuma kai hari: Miyagun yan bindiga sun hallaka akalla mutum 6, sun sace wasu da dama a jihar Katsina

Jihar Kaduna
Fusatattun jam'an gari sun sheƙe wani ɗan leken asirin yan bindiga da iyalansa a Kaduna Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A cewar rahoton, Abdullahi Muhammed Gobirawa, matarsa Binta Abdullahi da kuma ɗansu Hassan Abdullahi sun rasa ransu ne yayin da fusatattun mutanen suka mamaye gidansu.

Fusatattun mutanen sun ɗauki wannan matakin ne domin maida martani ga yan leƙe asirin musamman saboda yawaitar sace-sacen mutane a yankin.

Gwamna El-Rufa'i Ya yi Allah wadai

Bayan samun wannan rahoto ne, gwamna El-Rufa'i na jihar Kaduna ya bayyana rashin jin daɗinsa da wannan ɗanyen aikin.

Gwamnan ya kuma yi Allah wadai da kisan, inda ya jaddada cewa ta hanyar doka ne ya kamata a ɗauki mataki kan yan ta'adda.

"Ya kamata mutane su bar doka ta yi aiki akan masu aikata manyan laifuka, domin ɗaukar mataki a hannu zai jawo wata babbar matsala ne."

Wane mataki gwamnan ya ɗauka?

Kara karanta wannan

Mutum hudu sun mutu yayin da rikici ya barke tsakanin mutanen gari da fulani makiyaya a Kaduna

Gwamna Malam El-Rufa'i ya umarci hukumomin tsaro su gudanar da bincike akan abinda mutane suka aikata.

Bugu da kari, ya yi kira ga mutane da su cigaba da bin doka da oda, kada su shiga hurumin da ba na su ba.

A wani labarin kuma Wani Mutumi ya damfari malamin addini miliyan N1.2m, An gurfanar da shi gaban Kotu

Yan sandan sun gurfanar da mutumin ɗan kimanin shekara 45 a gaban kotu da tuhuma guda biyu a kansa.

Sai dai Taiwo yace sam bai aikata abinda ake zarginsa a kai ba, alkali ya bashi beli bisa wasu sharuɗɗa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262