Babbar Magana: Wani Mutumi ya damfari malamin addini miliyan N1.2m, An gurfanar da shi gaban Kotu

Babbar Magana: Wani Mutumi ya damfari malamin addini miliyan N1.2m, An gurfanar da shi gaban Kotu

  • Hukumar yan sanda ta damke wani mutumi, Taiwo Awopetu, da zargin damfarar wani malamin coci miliyan N1.2m
  • Yan sandan sun gurfanar da mutumin ɗan kimanin shekara 45 a gaban kotu da tuhuma guda biyu a kansa
  • Sai dai Taiwo yace sam bai aikata abinda ake zarginsa a kai ba, alkali ya bashi beli bisa wasu sharuɗɗa

Lagos - A ranar Talata, hukumar yan sanda reshen jihar Legas ta gurfanar da wani mutumi, Taiwo Awopetu, a gaban kotun Majistire.

Vanguard tace an gurfanar da mutumin ne ɗan kimanin shekara 45 bisa zargin damfarar wani malamin coci, Fasto Felix Ogoh, kudi kimanin miliyan N1.2m.

Wanda ake zargin dai yana fuskantar shari'a a kan abu biyu, damfara da kuma tuhumar sata.

Kotu a Legas
Babbar Magana: Wani Mutumi ya damfari malamin addini miliyan N1.2m, An gurfanar da shi gaban Kotu Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Ta ya mutumin ya damfari Faston?

Mai gabatar da ƙara, ASP Ikem Uko, ya shaidawa kotu cewa mutumin da ake zargin ya aikata laifin ne a watan Janairu 2021, a Ajara, yankin Badagry dake jihar Legas.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Uko ya bayyana cewa mutumin ya karɓi miliyan N1.2m daga hannun faston akan yarjejeniyar siyar masa da motar Toyota Corolla 2006.

Amma kawai wanda ke zargin ya karkatar da kuɗin zuwa amfanin karan kansa ba tare da karasa cinikin motar ba.

Mai gabatar da karan yace laifin da ya aikata ya saɓa wa sashi na 314 da 287 na kundin manyan laifuka na jihar Legas.

Shin mutumin ya amsa laifinsa?

A nasa ɓangaren, wanda ake zargi, Taiwo Awopetu, ya musanta tuhume-tuhumen da ake masa a gaban kotun.

Alkalin kotun, Patrick Adekomaiya, ya baiwa wanda ake zargin beli akan kudi N200,000 da kuma wasu mutum biyu da zasu tsaya masa.

Adekomaiya, ya bayyana cewa sharaɗi ne waɗan da zasu lamunce masa ya kasance mazauna yankin da kotun take ne kuma su gabatar da shaidar biyan haraji ga gwamnatin jiha.

Kara karanta wannan

Mutum hudu sun mutu yayin da rikici ya barke tsakanin mutanen gari da fulani makiyaya a Kaduna

Daga nan kuma sai ya ɗage zaman har zuwa 23 ga watan Nuwamba domin cigaba da sauraron shari'ar.

A wani labarin kuma Miyagun yan bindiga sun hallaka mutum 6, sun sace wasu dama a jihar Katsina

Rahoto ya nuna cewa maharan sun farmaki ƙauyen Unguwar Samanja a Faskari ana gab da sallar Magrib.

Wani mazaunin Daudawa ya koka kan yadda yan bindiga ke cigaba da aikin ta'addancinsu a Faskari duk da matakan da gwamnati ta ɗauka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262