'Yan bindiga: Sarkin Birnin Gwari ya bayyana alherin da katse hanyoyin sadarwa ya jawo
- Sarkin Birnin Gwari ya magantu kan kokarin da aka yi na dakile hanyoyin sadarwa a sassa daban na jihar Kaduna
- Ya ce, dakilewar ta haifar da da mai ido, domin kuwa hakan ya rage karfin 'yan bindiga tare da raunata ayyukansu
- Ya kuma bayyana dalilin da yasa wasu 'yan bindigan suka yi ta guduwa daga yankunan Zamfara zuwa Kaduna
Kaduna - Daily Trust ta ruwaito cewa, Mai martaba Sarkin Birnin Gwari a Jihar Kaduna, Alhaji Zubairu Jibril MaiGwari, ya ce rufe hanyoyin sadarwa ya raunana tare da rage karfin ‘yan bindigar da ke addabar jama’a a jihar.
Sarkin ya bayyana hakan ne a yayin wani taro da ma’aikatar tsaron da harkokin cikin gida ta jihar Kaduna ta shirya.
Ya ce matakan da gwamnati ta dauka na dakile ayyukan ‘yan bindiga na samar da sakamako mai kyau a sassan karamar hukumar Birnin Gwari.
A cewarsa, hare-haren da sojoji ke ci gaba da yi a Zamfara sun fatattaki wasu ‘yan bindigar zuwa sassan Birnin Gwari saboda yunwa.
A kalamantsa:
“Mafi yawansu (’yan bindigan) da aka fatattake su daga Jihar Zamfara sun dawo Birnin Gwari sun hana mutane noma. Yanzu idan suka sace wani, sai su ce masa ya zo ya kawo musu abinci."
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar ta Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce an dauki matakan dakile barnar ne domin kare lafiyar jama’a don taimakawa jami’an tsaro a yakin da suke yi da ‘yan bindiga.
An katse hanyoyin sadarwa a Kaduna
A baya, gwamnatin jihar Kaduna ta yanke shawarar katse hanyoyin sadarwa a wasu sassan jihar saboda yawaitar hare-hare na 'yan bindiga, ciki har da Birnin Gwari.
Channels Tv ta ruwaito cewa, gwamnati ta dauki wannan matakin ne domin durkusar da karfin 'yan bindiga a wasu sassan Kaduna.
Daga karshe, shugaba Buhari ya gano dalilai uku da suka jawo tabarbarewar tsaro
A wnai labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya ce abubuwa daban-daban ne suka jawo matsalar tsaro da kasar ke fuskanta.
Ya yi wannan jawabi ne a wani takaitaccen biki da aka yi a fadar gwamnati da ke Abuja, inda Jakadun Japan, Tarayyar Turai, Burundi, Denmark, Finland, Ireland, Cape Verde, Faransa, Qatar; da manyan kwamishinonin kasar Saliyo da Ghana suka karbi wasikun amincewa.
Ya ce ana bukatar karin hadin gwiwa domin shawo kan kalubalen rashin tsaro a kasar, Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng