Fusataccen miji ya garkame matarsa a cikin gida, ya cinna wuta yayin da suka samu sabani

Fusataccen miji ya garkame matarsa a cikin gida, ya cinna wuta yayin da suka samu sabani

  • Rahoto ya bayyana cewa faɗa ya kaure tsakanin miji da matarsa a jihar Legas har lamarin ya kai ga rasa rayuwar matar
  • Matar mai suna Ebere ta mutu ne bayan mijinta ya kulle ta a cikin ɗaki, sannan ya cinna wa ɗaƙin wuta
  • Makotan gidan sun tabbatar da haka, a cewar su shi kan shi mijin ya samu raunuka daga lamarin

Lagos - Wata mata mai suna Ebere, ta samu munanan raunuka na ƙuna lokacin da mijinta ya cinna wa gidan da suke zaune wuta daga samun saɓani.

Punch ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a layin Ifesowapo, yankin Asolo-Agbede, ƙaramar hukumar Ikorodu a jihar Legas.

Rahotanni sun bayyana cewa ma'auratan na zaune a cikin gidansu, lokacin da gardama ta shiga tsakaninsu har ta kai ga faɗa.

Layin da lamarin ya faru
Fusataccen miji ya garkame matarsa a cikin gida, ya cinna wuta yayin da suka samu sabani Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Yadda lamarin ya faru a tsakanin su

Kara karanta wannan

Mutum hudu sun mutu yayin da rikici ya barke tsakanin mutanen gari da fulani makiyaya a Kaduna

Cikin fushi, mijin ya kulle Ebere a cikin ɗaki, sannan kuma ya cinna wa ɗakin wuta.

Ebere ta dinga kururuwan neman taimako saboda radaɗin da take sha, yayin da mjin ya gaza jure kukan matarsa ya yi kokarin buɗe ta.

Matar, wacce ta ji raunukan ƙuna da ƙirjinta da sauran wasu sassan jikinta, an yi gaggawar kaita asibiti, inda likita ya tabbatar ta mutu.

Shin babu mutane ne a yankin?

Ɗaya daga cikin maƙotan gidan, wanda ya nemi a sakaya sunansa yace yana zaune a kofar gidansa lokacin da Ebere ta fito da gudu tana neman taimako.

Mutumin yace:

"Mun ga hanunta ya ƙone, amma tana kara nanata mana mu kaita asibiti, bayan mun kai ta asibiti ne muka gano cewa ƙirjinta ma ya ƙone."

Kara karanta wannan

Tsananin kishi ya sa saurayi ture budurwarsa har lahira a Bauchi

"Asibitin ne suka yi amfani da motar agaji wajen gaggauta mai da ita asibitin koyarwa na jami'ar jihar Legas domin a yi mata aiki."
"Bayan ta yi fama da jinya na tsawon mako ɗaya ne, aka tabbatar da mutuwarta a LASUTH."

Mutumin ya ƙara da cewa mijinta ne ya yi amfani da fetur wajen cinnawa gidan su wuta, kuma yana tsammanin shima ya samu raunuka.

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Kakakin yan sandan jihar, CSP Adekunle Ajisebutu, yace har yanzun babu wanda ya kawo musu rahoton faruwar lamarin.

"Na kira DPO na yankin domin tabbatar wa, amma ya faɗa mun cewa babu wani rahoto da aka kai musu makamancin haka."

A wani labarin kuma Yan bindiga sun kutsa wurin Ibada ana tsaka da bauta, Sun yi awon gaba da mutum 3

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun yi awon gaba da masu bauta mutum uku kuma sun nemi miliyoyin kuɗin fansa.

Kara karanta wannan

Kotu ta hukunta wata mata dake duba wayar mijinta ba tare da izini ba

Rundunar yan sandan jihar tace jami'anta sun bazama neman maharan tare da ceto mutanen da aka sace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262