Dattawan Arewa sun tafi kotu, sun bukaci a raba Najeriya, a ware 'yan wani yankin kudu

Dattawan Arewa sun tafi kotu, sun bukaci a raba Najeriya, a ware 'yan wani yankin kudu

  • Dattawan arewa sun nemi gwamnati ta amince da bukatar kudu maso gabas a raba ta da Najeriya
  • Wannan na zuwa ne ta hannun wasu dattijai da suka shigar da batun kotu don neman maslaha
  • A bangare guda, wasu lauyoyin kudu sun amince da hakan, sun bayyana goyon baya da jama'ar ta kudu

Abuja - Wata tawagar dattawa daga Arewacin Najeriya ta nemi babban kotun tarayya reshen Abuja da a roki 'yan majalisu a Najeriya su cire yankin kudu maso gabas daga Najeriya kafin aiwatar da gyare-gyaren kundin tsarin mulkin Najeriya.

Nastura Ashir Shariff, Balarabe Rufa’I, Abdul-Aziz Sulaiman da Aminu Adam sun shigar da batun kotu tare da bayyana cewa, hakan zai taimaka wajen rage faruwar rikice-rikice da zubar da jinane a daga 'yan awaren yankin.

Sun yi ikirarin cewa ba sa son a maimaita yakin basasar da aka yi a Najeriya tsakanin 1967 zuwa 1970 wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyin al’ummar kasar da yawansu ya kai biliyoyin Naira, Daily Sun ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja

Dattawan Arewa sun tafi kotu, sun bukaci a raba Najeriya, a ware 'yan wani yankin kudu
Taswirar Najeriya | Hoto: nnn.ng
Asali: Depositphotos

Wadanda ake magana akansu a cikin karar sun hada da Babban Lauyan Tarayya (AGF), Shugaban Majalisar Dattawa, Kakakin Majalisar Wakilai da Majalisar Dokoki ta Kasa.

Sai dai a wani martani na gaggawa, lauyoyin yankin kudu maso gabas masu magana da harshen Igbo a Najeriya sun nemi kotu ta hada su a jerin wadanda ake magana a kansu.

Lauyoyin da ke karkashin wani Babban Lauyan Najeriya, Cif Chuks Muoma, Ukpai Ukairo, Ebere Uzoatu da Hon Obi Emuka suna neman kotu ta ba su izinin shiga karar a matsayin wakilan al'ummar yankin Kudu maso Gabas.

Sun shigar da wannan batu a ranar Litinin ta hannun Victor Onweremadu ya shigar, inda suka bayyana cewa, bukatar dattawan Arewan ya dace da bukatarsu, Premium Times ta ruwaito.

Dangane da wannan bukata, kotu a karkashin mai shari'a Inyang Eden Ekwo ta sanya ranar 1 ga watan Nuwamba domin caccaka tsinke akai.

Kara karanta wannan

Makin CGPA 7.0: Jerin 'yan mata 5 da suka kafa tarihi a karatun jami'a a Najeriya

Yankin kudu ya jima yana fama da hare-haren 'yan IPOB, wata haramtacciyar kungiyar aware da ke fafutukar kafa kasar Biafra.

Jigo a kudu ya gano hanyar lallabar 'yan Arewa su mika mulki kudu a 2023

A wani labarin, Jaridar TheCable ta ruwaito cewa, Tunde Bakare, mai kula da cocin Citadel Global Community, ya ce duk wanda ke son jagorantar Najeriya dole ne ya tattauna da yankin Arewacin kasar.

Da yake magana a wata hira da ThisDay, Bakare ya ce yana shakkar idan Arewa za ta bar mulki cikin dadin rai.

Ya ce babu wani sashe na kasar "da zai iya cin zabe da kansa" saboda haka hadin gwiwa ne ya dace da nasarar zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.