Karin bayani: ISWAP ta hallaka wasu jiga-jigan kwamandojin Boko Haram da mabiyansu 18
- Gungun 'yan ta'addan ISWAP sun kai wa 'yan ta'addan Boko Haram hari a wani yankin jihar Borno
- Rahoto ya ce an hallaka wasu jiga-jigai daga cikin kwamandojin Boko Haram a kwanton baunar na ISWAP
- Hakazalika, wasu 15 daga cikin mambobin kungiyar duk su ma sun hallaka a harin na ranar Lahadi
Borno - Jaridar PRNigeria ta ruwaito cewa an kashe manyan jiga-jigan kungiyar Boko Haram guda biyu, Amir Modou Marte da Amir Moustapha Baga .
An kawar da su ne a wani kwanton bauna da mayakan abokan hamayyarsu na ISWAP suka yi a ranar Lahadi 24 ga watan Oktoba.
An tattaro cewa wasu 'yan ta'adda 15 na daga cikin wadanda kungiyar Boko Haram ta kashe a lokacin kwanton baunar da suka yi a Toumboun Gadura'a.
'Yan Boko Haram sun kai sabon hari Yobe, sun sha ruwan wuta a hannun sojojin Najeriya
Mayakan Boko Haram, a ranar Asabar 24 ga watan Oktoba, sun kai hari kan sansanin sojoji da ke kauyen Katarko da ke karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wasu majiyoyi sun shaidawa TheCable cewa maharan sun shiga kauyen Katarko ne a cikin manyan motocin yaki guda 10 sannan suka kai hari kan sojoji.
An ce sun fafata da jami'an tsaro da ke sansanin a musayar wuta da suka yi.
Sojoji na gina rugar Fulani a kudu: Rundunar soji ta yi martani kan jita-jita
A wani labarin, rundunar sojin Najeriya ta karyata jita-jitar da ke yawo mai cewa, a halin yanzu wata runduna na gina matsugunar Fulani a yankin kudu maso gabashin Najeriya.
Jerin Sunaye: Shugabannin Ƴan Ta’adda da Ƴan Bindiga Da Aka Kashe Daga Farkon Shekarar 2021 Zuwa Yanzu
Jita-jitar da ake yadawa ta ce, runduna ta 82 ta sojin Najeriya tana aikin gina rugar Fulani a tsakanin Ochima da Affa a cikin Igbo-Etiti da Udi na jihar Enugu.
A cikin wata sanarwar da Legit.ng Hausa ta samu a ranar Laraba 13 ga watan Oktoba dauke da sa hannun Manjo Abubakar Abdullahi, Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulda da Jama'a na Rundunar, rundunar sojin Najeriya ta watsi da batun.
Asali: Legit.ng