Ku tattauna da Igboho, IPOB kamar yadda na ke yi da 'yan bindiga, Gumi ga malaman kudu

Ku tattauna da Igboho, IPOB kamar yadda na ke yi da 'yan bindiga, Gumi ga malaman kudu

  • Sheikh Ahmad Gumi ya yi kira ga malaman Igbo da Yarabawa da su fara tattaunawa da masu tada kayar baya a yankunansu
  • Fitaccen malamin ya ce hakan ne kadai zai sa a shawo kan matsalar 'yan awaren IPOB da kuma Igboho na kasar Yarabawa
  • Malamin ya ce a halin yanzu matsalar kabilanci da ta mabanbanta addinai da akidu sun mamaye Najeriya, don haka sai da tattaunawa

Kaduna - Sheikh Ahmad Gumi ya bukaci malaman kudancin kasar nan da su tashi tsaye wurin tattaunawa da masu tada kayar baya tare da assasa rashin tsaro a yankunansu kamar yadda ya ke wa 'yan bindiga.

Fitaccen malamin ya sanar da hakan ne yayin da ya ke fitar da takarda kan martaninsa ga masu bukatar gwamnatin tarayya ta ayyana 'yan bindiga da 'yan ta'adda, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi: Za a yi nadamar ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda

Ku tattauna da Igboho, IPOB kamar yadda na ke yi da 'yan bindiga, Gumi ga malaman kudu
Ku tattauna da Igboho, IPOB kamar yadda na ke yi da 'yan bindiga, Gumi ga malaman kudu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A makon da ya gabata, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya sake bukatar gwamnatin tarayya da ta bayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda.

Tsokacin gwamnan ya janyo cece-kuce daga wurin jama'a daban-daban kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

A yayin duba wannan tsokacin, Gumi ya ce ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda ba shi ba ne hanyar shawo kan matsalar da arewa ta ke ciki.

"Kusan shekaru 12 ke nan yankin arewa maso gabas ya gigita da ta'addanci. Idan aka bar ta'addanci ya shigo cikin wadannan 'yan bindigan, arewa maso yamma za ta gurbace.
"Tuni dama 'yan awaren IPOB sun addabi yankin kudu maso gabas kuma Igboho ya shirya tsaf wurin gigita yankin kudu maso yamma. Ga wadanda ke son hargitsa arewa maso yamma, bismillah. Me ya rage a Najeriya kuma?

Kara karanta wannan

Tsoro da zaman dardar: Yadda shirin NYSC ya zama abin tsaro ga 'yan bautar kasa

"Na fara fitar da 'yan bindigan nan daga rashin wayewarsu amma abun takaicin shi ne mutane kadan ke taimakawa, sai da yawa da ke caccaka," yace.
"Ina fatan wasu malaman Igbo za su shiga cikin tsagerun IPOB kamar yadda na yi tare da tattaunawa da su. Wani faston kasar Oduduwa ya shiga wurin su Igboho ya san hanyar wayarwa da jama'a kai. Malaman addinai za su iya hakan.
“Abun takaicin shi ne yadda jama'a ke zaune a shararriyar inuwa suna tsokaci marasa kyau wadanda ke assasa matsalar kabilanci.
"A karni na 21, marasa ilimi sun cika kasar nan da kuma masu son kabilanci a komai, hakan ne ka assasa matsalar kabilanci.
"Najeriya kasa ce mai addinai da yawa, ko a addini daya kuwa, akwai dariku daban-daban wadanda babu zaman lafiiya da fahimtar juna a tsakanin mabanbantan darikun.
“Har yanzu Najeriya mafarki ta ke yi matukar za ta saka karfi ba tare da saka kwakwalwa ba wurin shawo kan matsaloli," yace a takardar.

Kara karanta wannan

Masari ya janye ra'ayinsa kan bindiganci, ya nemi a ayyana dokar ta-baci kan rashin tsaro

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng