Dama ta samu: Buhari zai ba masu digiri bashin miliyoyi saboda rage zaman banza
- Gwamnatin tarayya ta ce daliban da suka kammala karatun digiri a Najeriya za su iya samun lamuni har na naira miliyan biyar domin yaki da rashin aikin yi
- A cewar Babban Bankin Najeriya, wasu na iya samun kusan N25m a ayyukan hadin gwiwa da ayyukan kamfani
- Gwamnati ta ce wannan shirin na da nufin samar da wani sabon tsarin kudi wanda zai bunkasa samar da ayyukan yi
Babban Bankin Najeriya ya sanar da sabon shirin lamuni ga wadanda suka kammala karatun jami'a da kwalejojin fasaha da ke son kafa kasuwanci, yana mai cewa matakin wani bangare ne a kokarinsa na yaki da rashin aikin yi a kasar.
Bankin ya ce za a aiwatar da shirin lamunin ne a karkashin shirin sa na Tertiary Institutions Entrepreneurship Scheme (TIES).
A cikin wata sanarwa da babban bankin ya fitar ta shafinsa na Facebook ya ce:
“Babban bankin na CBN, a matsayin wani bangare na manufofin sa na magance hauhawar rashin aikin yi ga matasa da zaman banza, ya bullo da Tertiary Institutions Entrepreneurship Scheme (TIES) don samar da canji mai kyau tsakanin daliban da suka kammala karatun digiri na kwalejojin kimiyya da jami’o’i a Najeriya, daga neman ayyukan gwamnati zuwa kasuwanci. .
"Shirin na da nufin samar da sabon tsarin kudi wanda zai habaka samar da ayyukan yi, habaka kasuwanci, da tallafawa ci gaban tattalin arziki."
Lamunin zai kama daga Naira miliyan 5 a fannun ayyukan daidaikun mutane/kebabbun kamfanoni/kananan kamfanoni, zuwa miliyan 25 ga ayyukan hadin gwiwa/ayyukan cikakkun kamfanoni.
Ana sa ran masu neman lamunin na zabin farko su kasance sun kammala karatu daga kowace jami'a ta Najeriya ko kwalejin fasaha a cikin shekaru bakwai da suka gabata.
Kalli cikakken bayani daga sanarwar CBN:
Dalla-dalla: Matakai 5 da zaku bi wajen cike fom na shirin 'Nigeria Jubilee Fellows'
A wani labarin, Gwamnatin tarayya ta bude kafar cike fom na shirin Nigeria Jubilee Fellowship, shirin da aka tsara ga matasan da suka kammala NYSC a Najeriya, Premium Times ta ruwaito.
An bude kafar a ranar Litinin 6 ga watan Satumba ga masu sha'awar cike fom kuma tsarin zai gudana na makwanni shida, "tsakanin 6 ga Satumba zuwa 20 ga Oktoba, 2021."
Gidan talabijin na Channels ya ce, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da shirin a ranar Talatar makon jiya ya kuma bukaci matasa a Najeriya da su yi hobbasa wajen shiga shirin.
Asali: Legit.ng