Masari ya janye ra'ayinsa kan bindiganci, ya nemi a ayyana dokar ta-baci kan rashin tsaro

Masari ya janye ra'ayinsa kan bindiganci, ya nemi a ayyana dokar ta-baci kan rashin tsaro

  • Gwamna Masari na jihar Katsina ya magantu kan hanyar samun zaman lafiya a kasar nan
  • Ya nemi gwamnatin tarayya da ta ayyana dokar ta-baci a fannin tsaron kasar baki daya
  • Ya bayyana haka ne watanni bayan da ya yi inkrarin sanya dokar ta-baci da wasu 'yan majalisu suka nema

Katsina - Jaridar TheCable ta ruwaito cewa, gwamnan jihar Katsina Aminu Masari ya roki gwamnatin tarayya da ta kafa dokar ta-baci a kan rashin tsaro.

Bukatar tasa na zuwa ne watanni bayan da ya yi watsi da kiran da majalisar wakilai ta yi a watan Afrilu, inda suka nemi gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta-baci kan rashin tsaro.

Masari ya ja da baya, ya nemi FG da ta ayyana dokar ta-baci kan rashin tsaro
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Da yake magana bayan ganawa da Ibrahim Gambari, shugaban ma’aikata, a fadar shugaban kasa a ranar 29 ga Afrilu, Masari ya ce:

Kara karanta wannan

Sojoji kadai ba za su iya magance matsalolin tsaronmu ba – Tukur Buratai

“Ta yaya dokar ta-baci za ta magance matsalar? Kuna da halin da sojoji ke cikin dukkan jihohin tarayya, sannan ku tambayi kanku, nawa muke da su? Shin ba mu wuce gona da iri ba?”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma yayin da yake bayyana bude babban taron kwata-kwata na shekarar 2021 na taron ‘yan majalisun dokokin jihohin Najeriya a ranar Asabar, Masari ya bukaci gwamnatin tarayya da ta ayyana dokar ta-baci kan rashin tsaro.

Ya kuma nemi gwamnatin tarayya ta rungumi tattaunawa a matsayin wani bangare na kokarin magance kalubalen tsaro.

A kalamansa:

“A jihar Katsina, babbar matsalar mu ita ce matsalar tsaro da muke fuskanta a wasu sassan jihar. Tare da goyon bayan majalisar dokokin jihar, an samar da wasu tsare-tsare na doka, yayin da aka sake fasalin wadanda ake da su don magance kalubalen tsaro.
“Za a iya magance matsalolin rikice-rikice tare da kungiyoyin daban-daban ta hanyar tattaunawa da masu ruwa da tsaki da sauran kungiyoyin da abin ya shafa don gujewa asarar rayuka da lalata kadarori da ake fuskanta a sassa da dama na jihar da kasa.

Kara karanta wannan

Buhari: Ba zan huta ba har sai na tabbatar Najeriya ba ta fama da kalubalen tsaro

Ya kuma bayyana cewa, hukumomin tsaro na iyakar kokarinsu, amma akwai bukatar kara kokari domin dakile matsalolin tsaron kasar.

Ana ci gaba da samun hare-haren 'yan bindiga a wurare daban-daban na fadin kasar nan, duk da cewa gwamnati na ikrarin samun saukin lamarin.

Yayin da masu sharhi ke fadin ra'ayoyinsu kan batun matsalar tsaro, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya bayyana ce, shi zai iya gyara kasar, The Nation ta ruwaito.

Yadda 'yan bindiga sun sace wasu daliban ajin 'Nursery'

A wani labarin, Wasu ‘yan bindiga sun sace wasu daliban makarantar kasa da firamare a garin Akure, babban birnin jihar Ondo.

Jaridar Vanguard ta rahotocewa sace yaran da har yanzu ba a san ko su waye ba ya faru ne a yankin Leo, cikin garin Akure da misalin karfe 8 na daren Juma'a.

Rahotanni sun bayyana cewa masu garkuwar sun bi mahaifiyar yaran ne har gida.

Kara karanta wannan

PDP na bukatar mutane masu mutunci domin lashe zaben shugaban kasa a 2023 - Fintiri

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.