Wani babban malami ya ɗirkawa budurwa cikin shege daga zuwa neman addu'a

Wani babban malami ya ɗirkawa budurwa cikin shege daga zuwa neman addu'a

  • Wani limamin coci a jihar Ondo, ya shiga hannun yan sanda bisa zarginsa da yi wa wata budurwa ciki daga zuwa neman addu'a
  • Faston dai ya amsa laifinsa da farko, amma daga baya ya musanta tuhumar da ake masa, amma ya amince zai ɗauki nauyin mai cikin
  • A cewarsa bayan ta haihu ne za'a iya sanin gaskiyar waye uban jaririn ta hanyar kwajin kwayar halitta

Ondo - Wani babban malamin addinin kirista ya shiga hannun yan sanda bisa zarginsa da yi wa wata budurwa cikin shege.

Aminiya Hausa ta ruwaito cewa babban faston ya ɗirkawa budurwar yar shekara 16 ciki ne ta tsiya yayin da aka kaita ya mata addu'a a cocinsa.

Binciken yan sanda ya nuna cewa bayan ya tilasta mata yin amfani da ita a gida, ya kuma tasa ta zuwa kasuwa da daddare inda ya sake kwanciya da ita a karo na biyu.

Kara karanta wannan

Na sayar da diyata N150,000 ne don in biya kudin haya, Mahaifiya

Jihar Ondo
Wani babban malami ya ɗirkawa budurwa cikin shege daga zuwa neman addu'a Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Shin faston ya amsa laifinsa?

Babban malamin na addinin kirista ya amsa laifin da ake tuhumarsa a kai da farko amma daga bisani yace addu'a kawai ya mata kamar yadda aka bukace shi ya yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jawabinsa yace:

"Na fuskanci tana tsantsar bukatar addu'a, amma matsalar da na rinka samu wajen yin addu'an shine turjiya daga gare ta. Ban taɓa saduwa da ita ba."
"Da farko na amince da zargin ne saboda azabar yan sanda, amma na yarda zan ɗauki nauyin cikin da abinda zata haifa."

Meyasa malamin zai kula da mai cikin?

A jawabinsa, Faston yace zai ɗauki nauyin mai cikin har zuwa sanda zata haifi abinda ke cikinta.

A hasashensa wannan lokacin ne za'a je a yi gwajin kwayar halitta ta jaririn da aka haifa, daga nan za'a gano gaskiyar waye mahaifinsa.

Kara karanta wannan

Shugaban Turkiyya ya gargadi Buhari, ya ce ya kula da masu shirin juyin mulki

A wani labarin kuma Daruruwan fursunoni sun tsere yayin da miyagun yan bindiga suka fasa gidan yari a Oyo

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun yi amfani da manyan makamai wajen tilasta wa jami'ai tserewa, kuma su samu damar shiga.

A halin yanzun hukumomin tsaro sun shirya jami'ai domin taimakawa jami'an tsaron gidan gyaran hali wajen gano maharan da fursunoni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262