Buhari: Ba zan huta ba har sai na tabbatar Najeriya ba ta fama da kalubalen tsaro

Buhari: Ba zan huta ba har sai na tabbatar Najeriya ba ta fama da kalubalen tsaro

  • Shugaba kasa Buhari ya ce ba zai taba hutawa ba har sai mulkinsa ya shawo kan kalubalen tsaro a kasar nan
  • Buhari, wanda ya samu wakilcin ministan kimiyya da fasaha, ya ce gwamnatinsa ta samar da duk abinda ya dace wurin nakasa 'yan ta'adda
  • Shugaban kasan ya ce gwamnatinsa ta kammala ayyukan da shugabbanin baya suka bari tare da dasawa da wasu na more rayuwa a Najeriya

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa mulkinsa ba zai huta ba har sai kalubalen tsaron da Najeriya ke fuskanta a yanzu ta kawo karshe, Daily Nigerian ta ruwaito.

Buhari, wanda ya samu wakailcin ministan kimiyya da fasaha, Dr Ogbonayan Onu, ya sanar da haka ne a yayin gabatar da wani littafi mai suna "Standing Strong" wanda tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani ya rubuta a Abuja.

Kara karanta wannan

Majalisa za ta mika ƙudurin ayyana 'yan bindiga da 'yan ta'adda gaban fadar shugaban kasa

Buhari: Ba zan huta ba har sai na tabbatar Najeriya ba ta fama da kalubalen tsaro
Buhari: Ba zan huta ba har sai na tabbatar Najeriya ba ta fama da kalubalen tsaro. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC
"Muna cigaba da duba hanyoyi da tsarikan cigaba da nakasa dukkan wani karfin 'yan ta'adda a kasar nan," yace.

Ya ce gwamnati ta na cigaba da kirkiro hanyar hada kai tsakanin rundunar sojoji da wadanda ba sojoji wurin aiki tukuru domin yakar laifuka da masu laifi a cikin kasar nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buhari ya ce an samar da dukkan kayayyakin bukata wurin karfafawa rundunar sojin kasar nan guiwa wurin yaki da ta'addanci, Daily Nigerian ta wallafa.

Ya jinjina wa dakarun sojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro wurin kokarinsu na yaki da ta'addanci a kasar nan.

Shugaban kasan ya jinjinawa mawallafin littafin kan kokarinsa.

"Abun farin ciki ne yadda ya rubuta gogewar da ya samu a matsayinsa na shugaban majalisar dattawa domin wasu su amfana.
“Littafin zai zama mai matukar amfani ga duk wanda zai so karantar matsalolin kasar nan domin sanin tarihinsu," yace.

Kara karanta wannan

Shugaban Turkiyya ya gargadi Buhari, ya ce ya kula da masu shirin juyin mulki

Ya ce mulkin shi ya kammala ayyuka manya wadanda shugabannin baya suka bari kuma ya hada da yin sabbin kayayyakin more rayuwa domin samun cigaba a fadin kasa nan kamar su layikan dogo da tituna.

Buhari ya fara bincikar kwazon ministocinsa yayin da ake rade-radin zai kori wasu

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya bude taron kwanaki biyu na duba kwazo da ayyukan ministocinsa a Abuja yayin da ake ta rade-radin zai sallami wasu ministocin kan rashin kwazo.

Taron wanda ya samu halartar ministoci, manyan sakatarorin gwamnati da sauran manyan jami'an gwamnati, taro ne da aka shirya domin duba yanayin ayyukan manyan masu mukamai a gwamnati, The Nation ta wallafa.

A ranar 1 ga watan Satumban da ta gabata, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da sallamar ministocinsa biyu a taron majalisar zartarwa ta tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng