Da duminsa: Buhari ya fara bincikar kwazon ministocinsa yayin da ake rade-radin zai kori wasu

Da duminsa: Buhari ya fara bincikar kwazon ministocinsa yayin da ake rade-radin zai kori wasu

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da taron duba kwazon ayyukan ministocinsa yayin da ake tsaka da rade-radin zai fatattaki wasu
  • Shugaban kasan ya kaddamar da taron kwanaki biyun a Abuja wanda ya samu halartar ministoci, manyan sakatarorin gwamnati da sauransu
  • Majiyoyi da dama sun tabbatar da cewa akwai yuwuwar shugaban kasan ya yi amfani da sakamakon wurin sallamar wasu daga ciki

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya bude taron kwanaki biyu na duba kwazo da ayyukan ministocinsa a Abuja yayin da ake ta rade-radin zai sallami wasu ministocin kan rashin kwazo.

Taron wanda ya samu halartar ministoci, manyan sakatarorin gwamnati da sauran manyan jami'an gwamnati, taro ne da aka shirya domin duba yanayin ayyukan manyan masu mukamai a gwamnati, The Nation ta wallafa.

Kara karanta wannan

Buhari ya ce gwamnatinsa ta shirya za ta fara kera makamai saboda wasu dalilai

Da duminsa: Buhari ya fara bincikar kwazon ministocinsa yayin da ake rade-radin zai kori wasu
Da duminsa: Buhari ya fara bincikar kwazon ministocinsa yayin da ake rade-radin zai kori wasu. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

A ranar 1 ga watan Satumban da ta gabata, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da sallamar ministocinsa biyu a taron majalisar zartarwa ta tarayya.

Ministan wutar lantarki, Injiniya Saleh Mamman da ministan aikin noma da habaka karkara, Alhaji Sabo Nanono ya sallama yayin da ya sanar da cewa za a cigaba da hakan, The Nation.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyoyi daga fadar shugaban kasa sun ce akwai yuwuwar shugaban kasan ya na jiran sakamakon duba ayyukan ministocin kafin ya dauka mataki na gaba, wanda zai iya hadawa da sallamar wadanda basu nuna kwazo ba.

A yayin jawabi wurin bude taron a wani dakin taro na gidan gwamnatin tarayya, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zai tsaya tsayin daka cikin kwanaki biyun nan domin sauraron dukkan jimillar ayyukan ministocin na shekaru biyu da watanni da suka gabata.

Kara karanta wannan

Bayan korar ministoci biyu, Buhari ya gargadi ministocinsa kan aiki tukuru

Bayan kwanaki 37, Buhari ya yi shiru kan nadin sabbin ministoci daga Kano da Taraba

A wani labari na daban, kwanaki 37 bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fatattaki ministoci biyu, Sabo Nanono da Saleh Mamman kan rashin kwazo, har yanzu shiru ake ji.

Tun bayan sallamar ministocin biyu da aka yi a ranar 1 ga watan Satumba, manyan 'yan siyasan jihohin Kano da Taraba suna ta hango kujerun, Daily Trust ta ruwaito.

Duk da shugaban kasan ya sauya wa wasu ministoci ma'aikatu inda ya maye gurbin Nanono da Mamman, 'yan siyasan jami'iyyar mai mulki daga jihohin suke ta jajen tsaikon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng