Gobara ta tashi a dakin kwanan dalibai mata a jami’ar UNIMAID

Gobara ta tashi a dakin kwanan dalibai mata a jami’ar UNIMAID

  • Gobara ta tashi a dakin kwanan dalibai mata a jami’ar Maiduguri da ke jihar Borno
  • Mummunan al'amarin ya faru ne a ranar Alhamis, 21 ga watan Oktoba da misalin karfe 3:10 na rana
  • Hukumar jami'ar ta ce girki da wata daliba ke yi ne ya haddasa gobarar, inda daki daya abun ya shafa

Maiduguri, jihar BornoAn yi asarar kayayyaki da dama yayin da gobara ta barke a daya daga cikin dakunan kwanan dalibai mata na jami’ar Maiduguri, a ranar Alhamis, 21 ga watan Oktoba.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa gobarar ta fara ne da misalin karfe 3:10 na rana a dakin kwanan dalibai mai suna Aisha Buhari.

Gobara ta tashi a dakin kwanan dalibai mata a jami’ar UNIMAID
Gobara ta tashi a dakin kwanan dalibai mata a jami’ar UNIMAID Hoto: Aminiya
Asali: UGC

An tattaro cewa gobarar ta lalata takardun dalibai, kayayyaki, ginin dakuna da kuma wasu kayayyaki.

Kara karanta wannan

Sai mun hada kai ne za mu iya cin galaba a kan miyagu – APC kan harin jirgin kasa

Rahoton ya kuma nuna cewa har yanzu ba a san musababbin gobarar ba.

An kuma rahoto cewa sai da ya dauki hukumar kashe gobara ta jami’ar, jami’an tsaro da dalibai kimanin awa daya kafin suka iya kashe gobarar.

Wata daliba da ke zaune a daya daga cikin dakunan da suka yi gobarar, wacce ta nemi a sakaya sunanta ta yi korafin cewa babu abun da ta iya dauka daga cikin kayayyakinta domin duk sun kone.

Ta ce:

“Ban iya tsiratar da komai ba, dukka kayana sun kone harda takarduna.

Daliban sun yi zargin cewa rashin isasshen ruwa a kusa yana daga cikin abun da ya kawo tsaiko wajen kashe gobarar cikin sauki.

Da take martani kan lamarin, hukumar makarantar ta ce ba a rasa rai ba inda ta ce an shawo kan lamarin.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Ba mu da tabbacin farmakin 'yan ta'adda ne, MD na NRC ya magantu

Aminiya ta rahoto cewa Sanarwar da Jami’in Hulda da Jama’a na Jami’ar Maiduguri, Farfesa Danjuma Gambo, ya fitar ta ce gobarar ta ci daki daya a daya daga cikin gine-ginen dakunan kwanan daliban, amma ba a samu rauni ba, ballantana asarar rai.

Ya ce:

“Gobarar ta shafi daya daga cikin dakunan ne sannan ba a rasa rai ko jin rauni ba. Binciken farko ya nuna cewa wata daliba ce ke girki lokacin da lamarin ya afku.
“Hukumar jami’ar na gudanar da bincike a yanzu haka domin gano musababbin gobarar.”

Babbar Magana: Sakateriyar Babban Birnin Tarayya Abuja Ta Kama da Wuta

A wani labarin, mun kawo a baya cewa wani ɓangare na sakateriyar babban birnin tarayya Abuja dake a Zone 3, cikin birnin Abuja ya kama da wuta yanzu haka, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Rahotanni dake fitowa yanzun haka sun tabbatar cewa babu wani cikakken bayani game da musabbabin kamawar wutar.

Kara karanta wannan

Jami’an DSS, ‘yan sanda, sojoji sun kewaye kotun Abuja a shari’ar Nnamdi Kanu

Hakanan kuma, gobarar ta shafi wasu daga cikin motocin dake harabar sakateriyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng