Bincike: 'Yan ta'addan ISWAP da Ansaru ne suka sanya bam a layin dogon Abuja zuwa Kaduna
- 'Yan ta'addan ISWAP tare da Ansaru ne ke da alhakin lalata layin dogon Abuja zuwa Kaduna
- Kamar yadda majiyoyin tsaro suka tabbatar, an ga hatimin kungiyoyin biyu a wuraren da suka kai farmakin
- Wata majiyar tsaro ta kara da cewa 'yan ta'addan sun so halaka rayukan mutanen jirgin ne
Kaduna - 'Yan ta'addan kungiyar ta'addancci ta ISWAP tare da Ansaru ne suke da alhakin lalata layin dogon Abuja zuwa Kaduna, majiyoyi masu karfi na tsaro suka tabbatar wa da Daily Trust a ranar Alhamis.
Karaikainar jiragen kasa daga Abuja zuwa Kaduna ta gurgunta na wucin-gadi daga daren Laraba zuwa Alhamis bayan an gano cewa 'yan ta'adda sun sanya bam tare da tashin wani sashi na layin dogon.
Miyagun sun koma da sa'o'in farko na ranar Alhamis inda suka sake lalata wani sashi na layin dogon, lamarin da yasa hukumar jiragen kasa ta Najeriya ta dakatar da ayyukan ta.
Duk da NRC ta kwatanta lamarin da barnar mabarnata masu son lalata kayayyakin hukumar, majiyar tsaro mai karfi ta ce da hannun 'yan ta'adda a lamarin.
Wani babban jami'in tsaro ya tabbatar wa da Daily Trust cewa, a cikin kwanakin da suka gabata, jami'an tsaro sun tare da halaka wasu 'yan ta'addan da suka yi yunkurin saka bam a gadoji da layikan dogo a Kaduna.
"Wannan farmakin su na da hatimin ISWAP da Ansaru, 'yan bindiga sun so sace mutane tare da bukatar kudin fansa amma wannan ta'addanci ne a bayyane," yace.
“Sun so kashe mutanen da ke jirgin kasan. Amma muna godiya ga Ubangiji da ba su yi nasarar ba," yace.
Wata babbar majiyar tsaro ta tabbatar da cewa a cikin kwanakin nan, jami'an tsaro sun samu labarin cewa an yi kokarin tashin layin dogo da bam amma suka dakile.
Daily Trust ta ruwaito cewa yayin gabatar da rahoton tsaro na watanni uku a ranar Laraba, gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa ana samun yaduwar bayanai tsakanin 'yan ta'adda da 'yan bindigan jihar.
Ba mu da tabbacin farmakin 'yan ta'adda ne, MD na NRC ya magantu
A wani labari na daban, manajan daraktan hukumar jiragen kasa ta Najeriya, NRC, Fidet Okhiria, ya musanta rade-radin da ke ta yawo na cewa 'yan ta'adda sun kai wa jirgin kasa tsakanin Abuja zuwa Kaduna farmaki.
Okhiria wanda ya zanta da Daily Trust ta wayar salula, ya tabbatar da cewa wani sashi na layin dogon ne aka lalata.
Sai dai, ya alakanta lamarin da mabarnata masu lalata kayan gwamnati inda ya ce ana bincike domin bankado abinda ya faru.
Asali: Legit.ng