Shugaban wurin aiki ya ba na ƙasa da shi da ke tattaki zuwa wurin aiki kyautar mota

Shugaban wurin aiki ya ba na ƙasa da shi da ke tattaki zuwa wurin aiki kyautar mota

  • Bayan motar wani matashi, Carr Walter ta samu matsala ana gobe zai fara zuwa aiki, daga nan ya yanke shawarar yin tattaki
  • Don kwashe mil 20, daga gidan sa zuwa wurin aikin, tun tsakar dare ya fara tattakin, sai karfe 4am ya kai mil 14 kafin a taimaka ma sa
  • Mutane da dama sun tausayawa wa halin da ya shiga ciki akan saboda dagewa da jajircewar sa akan aikin sa

Wani matashi, Walter, ya yi tattakain mil 20 a ranar sa ta farko ta zuwa wurin aiki. Motar sa ta samu matsala ana gobe zai fara zuwa aikin hakan ya sa ya yanke wannan shawarar.

Kafin safiyar, ya yi kokarin tuntubar abokan sa amma babu alamar zai samu tallafi saboda ya sanar da su a kurarren lokaci kamar yadda Understanding Compassion ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kira wayar wani a coci, ya fito sun bindige shi sun gudu

Shugaban wurin aiki ya ba na ƙasa da shi da ke tattaki zuwa wurin aiki kyautar mota
Matashin ya zubar da hawayen farin ciki yayin da aka bashi kyautar motan. Photo source: Understanding Compassion
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga nan ne ya yanke shawarar fara tattaki tun karfe 12am don isa wurin aikin da wuri. Matashin bai bari rashin abin hawan ya dakatar da shi ba.

Bayan duba taswira ne ya gane cewa a kalla sai ya kwashe sa’o’i 7 kafin ya isa Pelham, daga nan ne ya yanke shawarar fara tafiyar tun tsakar dare.

Ya kwashi baccin sa da rana sannan ya falka tsakar dare da misalin karfe 12am ya fara tattakin, kamar yadda New York Post ta ruwaito.

Kamar yadda ya bayyana:

“Ina so in isa kafin karfe 8am. Kuma ina so inyi asubancin ne don kamfanin su gane cewa da gaske na ke.”

Bayan sa’o’i 4 da fara tattakin ya kasa ci gaba

Da misalin 4am, matashin ya yi tattakin mil 14, saura mil 6 kenan, don haka ya yanke shawarar zama ya huta. Anan ya ce duk cikin sa ya fara ma sa ciwo.

Kara karanta wannan

Dan achaba ya tsinta N20.8m a titi, ya samu tukuicin N600k bayan ya mayar wa masu kudin

Daga baya ya samu taimakon ‘yan sanda wadanda su ka gan shi a bakin titi su ka tausaya ma sa bayan jin labarinsa.

Sun taimaka ma sa da karin kumallo sannan su ka ajiye shi a wani wuri don ya huta. Daga nan wani dan sanda ya kai shi har wurin aikin.

Bayan isar sa wurin aikin ne mutane da dama su ka yi mamakin irin wannan jajircewar ta Walter daga nan labarin sa ya yadu a yanar gizo.

Bayan shugaban sa na wurin aiki ya samu labarin ne ya yi mamaki kuma ya tallafa ma sa da mota.

Saidai tun kafin nan masoya da masu ma sa fatan alheri sun tara ma sa kudade kafin isowar motar ta wurin shugaban sa.

Anan ne mutane su ka dinga tsokaci karkashin wallafar labarin sa, inda wani Noey NoEy Pamindua yace:

“Labari mai ban al’ajabi, ina ma sa fatan alheri.”

Julie Horn kuwa cewa ta yi:

Kara karanta wannan

Na yi gyaran kwata ana biya na N20: Ɗan kwallo mafi tsada a Afirka kuma tauraron Super Eagles, Victor Osimhen

“Ban san wannan matashin ba amma ina alfahari da shi kuma ina ma sa fatan dorewar daukaka da farin ciki.”

William Messhias Wallace ya ce:

“Barka, duniya ta na bukatar shugabannin a wurin aiki irin wannan. Ubangiji ya taimaka mu ku gaba daya.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164