Sai mun hada kai ne za mu iya cin galaba a kan miyagu – APC kan harin jirgin kasa

Sai mun hada kai ne za mu iya cin galaba a kan miyagu – APC kan harin jirgin kasa

  • Jam'iyyar APC mai mulki ta yi Allah wadai da harin da mabarnata suka kai kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna
  • APC ta ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na iya bakin kokarinta domin inganta rayuwar 'yan Najeriya, amma dole sai an hada kai don ganin bayan 'yan hana ruwa gudu
  • Wasu da ake zaton 'yan bindiga ne sun kai hari kan jirgin kasa a daren ranar Laraba, 20 ga watan Oktoba

Abuja - Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta ce sai dukka ‘yan Najeriya sun hada hannu idan ana son ganin bayan masu ta’adi a kasar nan.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa jam’iyyar mai mulki na martani ne ga harin da wasu da ake zaton ‘yan bindiga ne suka kai kan jirgin kasa a layin dogo na Abuja zuwa Kaduna.

Kara karanta wannan

Muna cikin tafiya sai muka ji kara - Fasinjojin jirgin da aka kai wa hari sun bayyana halin da suka shiga

Sai mun hada kai ne za mu iya cin galaba a kan miyagu – APC kan harin jirgin kasa
Sai mun hada kai ne za mu iya cin galaba a kan miyagu – APC kan harin jirgin kasa Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

An yi zargin cewa ‘yan bindiga sun dasa bam ne a hanyar jirgin, wanda yayi sanadiyar tsayawar jirgin kasan a hanyar Abuja zuwa Kaduna a daren Laraba, 20 ga watan Oktoba. Lamarin ya afku ne da misalin karfe 8:00 na dare.

A jawabin da ya fitar a ranar Alhamis, 21 ga watan Oktoba, John Akpanudoedehe, sakataren APC na kasa, ya bayyana harin a matsayin abun Allah wadai. Sai dai ya ce za a iya kawo karshen lamarin ta hanyar hada kai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

“Zuwa yanzu ‘yan Najeriya sun gano cewa gwamnatin APC da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke jagoranta na nufin su da alkhairi kuma tana yin iya bakin kokarinta domin samar da ababen more rayuwa a yayin da ake tsaka da wahalar tattalin arziki a duniya.
“Dole sai mun hada kai domin cin galaba kan masu barna wadanda suka sha alwashin komar da Najeriya baya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Nnamdi Kanu ya musanta zargin da ake masa a gaban kotu

“A safiyar nan ne, miyagu suka kai hari kan fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, suna hana ‘yan Najeriya cin moriyar ababen da aka tanadar. Wannan abun bakin ciki ne, amma a tare za mu kawo karshen su.”

Ba mu da tabbacin farmakin 'yan ta'adda ne, MD na NRC ya magantu

A gefe guda, Manajan daraktan hukumar jiragen kasa ta Najeriya, NRC, Fidet Okhiria, ya musanta rade-radin da ke ta yawo na cewa 'yan ta'adda sun kai wa jirgin kasa tsakanin Abuja zuwa Kaduna farmaki.

Okhiria wanda ya zanta da Daily Trust ta wayar salula, ya tabbatar da cewa wani sashi na layin dogon ne aka lalata.

Sai dai, ya alakanta lamarin da mabarnata masu lalata kayan gwamnati inda ya ce ana bincike domin bankado abinda ya faru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng