Muna cikin tafiya sai muka ji kara - Fasinjojin jirgin da aka kai wa hari sun bayyana halin da suka shiga
- Matafiya da ke cikin jirgin kasa na Kaduna-Abuja da aka kai wa hari sun bayyana halin da suka tsinci kansu a ciki
- Lamarin ya afku ne bayan jirgin wanda ya tashi da karfe 6:00 na yamma ya hadu da cikas a ranar Laraba, 20 ga watan Oktoba
- Sun bayyana cewa sun ji wani kara kafin jirgin ya tsaya cak, inda suka shafe tsawon awa hudu a dajin Allah
Kaduna - Fasinjojin jirgin da ake zaton 'yan bindiga sun kai wa hari a daren ranar Laraba, 20 ga watan Oktoba a hanyar Kaduna zuwa Abuja sun bayyana halin da suka shiga.
Matafiyan sun bayyana cewa sai da suka shafe kimanin awa hudu a cikin dajin Allah inda suka yi cirko-cirko ba tare da sanin madafa ba.
Daily Trust ta rahoto cewa an ja jirgin kasan, wanda shine tashin karshe na ranar, zuwa tashar jirgin kasa na Rigasa da misalin karfe 2:00 na tsakar dare bayan an turo sabon jirgi daga tashar Idu da ke Abuja domin ceto fasinjojin da suka yi cirko-cirko.
Tsohon shugaban Kungiyar NUJ a Kaduna, Garba Mohammed, wanda ya kasance a cikin jirgin ya ce sun shiga halin fargaba domin daga fasinjoji sai yan tsirarun Jami’an ‘yan sanda ne a wajen.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa nisan wurin ya kai kimanin kilomita 40 zuwa tashar Rigasa.
Ya kuma ce komai na tafiya daidai a lokacin da jirgin ya tashi daga Abuja amma kafin ya kai masaukinsa na karshe a Rigasa, sai suka ji wani kara sannan sai jirgin ya tsaya a hankali.
Ya ce:
“Sai wutan ya mutu, na’urar AC ya daina aiki sannan aka rufe mu a cikin jirgin. Babu sabis, babu ruwan sha, haka mutane suka koma shan ruwa daga fanfon bandaki sai gashi bandakin ya kacame.
“Kimanin kilomita 40 zuwa Kaduna, sai muka ji kara sannan Jami’an tsaro suka nemi mu fake. Bayan yan mintoci kadan, sai Jami’an tsaro suka dunga sintiri. Sai da muka bude tagogi saboda zafi sannan mu iya ganin hanya daga inda jirgin ya tsaya.”
Sai dai kuma ya yi bayanin cewa akwai tsaro daga rundunar soji wadanda suka yi masu rakiya zuwa tashar jirgin Rigasa bayan sa’o’i hudu a cikin sabon jirgi.
“Sabon jirgin baya gudu don haka muka shafe tsawon sa’o’i 2 a tafiyar minti 30. A lokacin da muka isa tashar Rigasa, mun tarar da mutane da dama cikin fargaba suna jiran ‘yan uwansu.”
Da aka tambaye shi ko ‘yan bindiga ne suka kai masu hari, Mohammed ya ce:
“Wasu mutane sun ce hari aka kai wa jirgin, amma bamu fuskanci wani barazana ba iya lokacin da muka shafe a tsaye, wanda ya kai kimanin awa hudu.
“Idan har wani zai iya kai hari kan jirgin sannan ya dakatar da shi na kimanin awa hudu, toh lallai suna da isasshen lokacin gano inda jirgin yake da kai masa hari, mun kasance karkashin kulawar ‘yan tsirarun Jami’an tsaro kafin muka tafi amma babu wanda ya kai mana hari.”
Rahoton ya kuma kawo cewa wata matafiya, Josephine Isiaku, ta yi bayanin cewa sun shafe tsawon awa hudu a inda basu sani ba, ma’aikatan jirgin da Jami’an tsaro basu yi masu bayanin halin da ake ciki ba inda tace hakan ya sanya su cikin tsoro da fargaba.
'Yan bindiga sun saka Bam a layin dogon Abuja/Kaduna, Shehu Sani ya tsallake rijiya da baya
A gefe guda, mun kawo cewa tsohon sanata da ya wakilci yankin Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya tsallake rijiya da bayan wasu ‘yan bindiga sun far masu a hanyar jirgin kasa.
Shehu Sani wanda ya bayyana halin da ya tsinci kansa a ciki a shafinsa na Facebook, ya ce ya shiga jirgin kasa a safiyar yau Alhamis, 21 ga watan Oktoba, sai kawai jirgin nasu yayi karo da wani abun fashewa da ‘yan bindigar suka dasa a kan hanya.
Sani ya ce ta kai har jirgin ya kusan sauka daga layinsa, ba don Allah ya takaita lamarin ba.
Asali: Legit.ng