Yadda mai SaharaReporters ya sha duka a hannun 'yan daba a harabar kotun Abuja

Yadda mai SaharaReporters ya sha duka a hannun 'yan daba a harabar kotun Abuja

  • Rahoto ya bayanna cewa, wasu 'yan daba sun lakadawa Sowore duka a harabar kotun Abuja
  • Sowore tare da wasu 'yan jarida sun bayyana a harabar kotun don sanin yadda za ta kaya a shari'ar Nnamdi Kanu
  • Rahoto ya bayyana yadda lamarin ya faru, da kuma yadda jami'an tsaro suka shiga tsakani

Abuja - Wasu da ake zargin 'yan daba ne sun kai hari ga mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore a babban kotun tarayya da ke Abuja ranar Alhamis 21 ga watan Oktoba.

Jami’an tsaro sun hana Sowore shiga kotun. Amma yayin da yake magana da jami'an tsaro, wasu yara maza kimanin 20, an lura sun iso wurin, The Nation ta ruwaito.

An lura da kasancewar su a cikin rudani saboda sun yi kama da 'yan neman rikici.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Nnamdi Kanu ya bayyana a gaban kotu, an hana 'yan jarida shiga

Yanzu-Yanzu: 'Yan daba sun lakadawa Sowore duka a wurin shari'ar Nnamdi Kanu
Mawallafin jaridar SaharaReporters, Sowore | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: Facebook

Amma ga mamakin kowa, jami'an tsaro sun yi shiru kan abin da ke faruwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Nan da nan wadanda ake zargin 'yan daban ne suka sauka kan Sowore, suka mare shi tare da kumsa mashi naushi.

Jami'an tsaro sun ga abin da ya faru sannan suka shiga tsakani bayan sun yi ihu ga wadanda ke wurin ta hanyar dakatar da Sowore.

Sai dai 'yan daban bayan sun daki Sowore sun tafi ba tare da jami’an tsaro sun musu komai ba.

Wannan ya haifar da wani tashin hankali yayin da mutanen da ke kusa suka bukaci a kama su.

Daga nan sai jama'a suka bi 'yan daban don kamo su yayin da jami'an tsaro ke kallon abin da ke faruwa.

Lokacin da lamarin ya dagule, jami'an tsaro sun shiga tsakani tare da rike wasu mutane biyu.

Kara karanta wannan

An ba mata masu ciki, masu shayarwa damar NYSC a garuruwan mazajensu

Martanin jami'an tsaro ya haifar da rade-radin cewa 'yan daban sun fito daga tsagin gwamnati ne

Kafin faruwar lamarin, Sowore ya ce:

“Zaman kotu ba zai cika ba har sai mutane suna wurin don shaida shari’ar. Ina so in zauna a gaban alkali in shaida komai.
“Su tabbatar mana cewa Kanu zai samu adalci. Abokina ne kuma ya kamata in kasance anan. Amma har yanzu hukumomin tsaro ba su ba ni damar shiga ba. ”

Bayan rikicin 'yan daban, jami'an tsaro sun fusata sun fatattaki kowa har da 'yan jarida.

Sun bugi wasu manema labarai da sanduna tare da tura wasu gefe.

Jami'an tsaron sun yi barazanar fasa kyamarorin wasu 'yan jarida da sauran mutanen da ke daukar lamarin.

Har ma sun tilasta wasu mutane su goge bidiyonsu da hotunansu.

Sun kori kowa daga kusa da kotun face wasu 'yan jaridar da suka ki tafiya.

Jami’an DSS, ‘yan sanda, sojoji sun kewaye kotun Abuja a shari’ar Nnamdi Kanu

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar EndSARS da barkonon hayaki

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa, an girke jami’an tsaro da yawa a babbar kotun tarayya da ke Abuja don shari’ar Nnamdi Kanu, jagoran kungiyar ‘yan asalin yankin Biafra ta IPOB.

An ga jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), rundunar sojan Najeriya da jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya suna gadin kowace kofar shiga kotun da titunan da ke shiga ginin kotun.

Ba a bar 'yan jaridar da sunayensu ba sa cikin jerin shirye-shiryen ba a kusa da harabar kotun, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kotu ta dage shari'ar Nnamdi Kanu, jami'an DSS sun iza keyarsa

Daga karshe, Jami'an tsaron farin kaya, DSS su sake iza keyar Nnamdi Kanu, shugaban 'yan awaren IPOB zuwa ma'adanarsu.

An gurfanar da Nnamdi Kanu a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja kan zargi bakwai da gwamnatin tarayya ke masa a ranar Alhamis, Daily Trust at ruwaito.

Kara karanta wannan

EndSARS: Yan sanda sun damke dan jaridar Legit a LekkiToll Gate

Kamar yadda TheCable ta wallafa, Kanu ya musanta zargin da ake masa da suka hada da cin amanar kasa da kuma ta'addanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.