An ba mata masu ciki, masu shayarwa damar NYSC a garuruwan mazajensu

An ba mata masu ciki, masu shayarwa damar NYSC a garuruwan mazajensu

  • Hukumar NYSC ta ba mata masu juna biyu damar zama a garuruwansu don zaman sansani
  • Hakazalika mata masu shayarwa ma an dauke musu jigilar barin garuruwansu saboda dalilai
  • NYSC ta kuma bayyana cewa, za ta dauki dukkan matakai don ganin an magance yaduwar Korona

Jaridar Guardian ta ruwaito cewa, dukkan matan aure masu juna biyu da masu shayarwa wadanda ba a tura su garuruwan mazajen su ba za su iya ci gaba da zuwa sansanin NYSC a jihohin da suke zaune, in ji hukumar NYSC.

NYSC, duk da haka, Ta ce dole ne mata masu juna biyu ko masu shayarwa su halarci shirin don yin rajista tare da wasu cike-ciken takardun da suka hada da, shaidar aure, takardar shaidar mazaunin miji da sauransu.

Da dumi-dumi: An ba mata masu ciki da masu shayarwa damar yin NYSC a garuruwansu
Shirin bautar kasa na NYSC | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Darakta-Janar na NYSC, Birgediya-Janar Shuaibu Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa kan atisayen shakarar 2021, Batch C Stream 1 wanda aka fara ranar Laraba a dukkan sansanoni 37 a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Kotu ta dage shari'ar Nnamdi Kanu, jami'an DSS sun iza keyarsa

Darakta janar ya yi bayanin cewa sabon batun an yi shi nedon rage wa mata nauyi, yana mai cewa NYSC “kungiya ce mai fuskar mutum.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Darakta janar din, wanda daraktar yada labarari da hulda da jama'a na NYSC, Misis Adenike Adeyemi ta wakilta, ya dage cewa membobin bautar kasa da jami'an sansanin da aka gwada basu da Korona ne za su sami shiga sansanin.

A cewar DG, jami'ai daga Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) za su kasance a sansanonin 37 yayin atisayen.

Hakazalika, ya bayyana cewa, hukumar tana yin mai yiwuwa wajen ganin an kange mutane daga kamuwa da cutar Korona a sansanonin ta hanyoyi da yawa.

A lokuta da dama an samu yaduwar Korona a sansanin NYSC, lamarin da ya jawo daukar matakan kariya.

A baya an samu mutane da dama da suke dauke da cutar ta Korona daga jihohin da nau'in Korona na Delta ya barke, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Yadda mawallafin ShaharaReporters ya sha duka a hannun 'yan daba a harabar kotun Abuja

Annobar Korona ta barke a sansanin NYSC na jihar Gombe

A baya kadan, akalla membobin bautar kasa 25, ciki har da mai shayarwa, suka kamu da cutar Korona a sansanin NYSC na jihar Gombe da ke Amada, Karamar Hukumar Akko.

Da yake tabbatar da lamarin a ranar Asabar a wata tattaunawa ta musamman, Kwamishinan Lafiya, Dakta Habu Dahiru, ya ce an yi wa masu yi mutane 25 gwaji a cikin kwanaki ukun da suka gabata, Punch ta ruwaito.

Ya kara da cewa an tura su zuwa cibiyar killacewa mallakar jihar a cibiyar cututtuka na Idris Mohammed da ke Kwadon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.