Sabbin kyawawan hotunan Shugaba Buhari da uwargidansa, Aisha sun bayyana
- Sabbin kyawawan hotunan Shugaban kasa Muhammadu Buhari da uwargidansa, Hajiya Aisha sun bayyana
- An gano shugaban kasar tare da mai dakinsa suna yi wa juna kallon kauna yayin da take gyara masa takunkumin fuska
- Wadannan hotuna sun birge mutane da dama inda suka tofa albarkacin bakunansu
Wasu kayatattun hotuna na shugaban kasa Muhammadu Buhari da uwargidansa, Hajiya Aisha Buhari sun bayyana.
A cikin hotunan wadanda suka ja hankalin ‘yan Najeriya da dama, an gano shugaban kasar da mai dakinsa cikin wani yanayi da ba kasafai ake gani ba.

Source: Facebook
Uwargidan Shugaban kasar ta kasance tana gyara masa takunkuminsa na fuska yayin da suke yi wa juna kallon kauna dauke da murmushi a fuskokinsu.
Hadimin Shugaban kasa a shafukan sadarwa na zamani, Bashir Ahmad ne ya yada hotunan a shafinsa na Facebook.
A saman hoton Bashir ya rubuta:
“Dan takaitaccen labari. Shugaban kasa da Uwargidan Shugaban kasa.”
Wadannan hotuna sun burge mutane da dama inda suka tofa albarkacin bakunansu
Legit.ng Hausa ta zakulo maku Wasu daga cikin martanin a kasa:
Muhammed Musa Kandi ya yi martani:
"Kyakkyawan iyali ."
Saminu Yusuf Abdullahi ya rubuta:
"Baba harda lumshe ido"
Aliyu Al Ameen Omar
"Baba na murmushi"
Buhari zai karba bakuncin shugaban kasar Turkiyya, Erdogan da matarsa
A gefe guda, mun kawo a baya cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai karba bakuncin shugaban kasa Recep Tayyip Erdogan na kasar Turkiyya na tsayin kwana biyu a ziyarar da ya kawo wa Najeriya daga Talata 19 ga watan Oktoba.
Wannan na kunshe ne a wata takarda da babban mataimakin shugaban kasa na musamman a fannin yada labarai, Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Talata.
Shugaban kasan ya samu rakiyar matarsa, Emine Erdogan, kuma zai shigo ta kasar Angola ne sannan ya karasa kasar Togo domin kammala ziyararsa.
Asali: Legit.ng

