Ganawar Buhari da shugaban Turkiyya: Abubuwa 5 da Najeriya za ta mora a ganawar
Ganawar Shugaba Muhammadu Buhari da Shugaban Kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, a ranar Laraba, 20 ga Oktoba, a Fadar Shugaban Kasa ya haifar da fa'ida ga juna wanda zai gudana cikin kankanin lokaci.
A cikin wani taron manema labarai bayan ziyarar, Shugaba Buhari ya bayyana cewa ya shiga tattaunawa mai matukar muhimmanci kan wasu batutuwan da suka shafi kasashen biyu, da nufin karfafa dankon zumunci tsakaninsu.
A cewar Buhari, muhimman batutuwan sun shafi yarjejeniyar da aka kulla tsakanin kasashen biyu wato MoU.
Wasu daga cikin fannoni a Najeriya da sabbin yarjejeniyoyi takwas da aka sanya hannu akai za su yi tasiri kamar haka:
- Makamashi
- Masana'antar Tsaro
- Tsaro
- Ma'adinai
- Sindarin HydroCarbons
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Haka kuma, gwamnatin tarayya ta amince ta cire Turkiyya daga cikin jerin sunayen kasashen da ta hana zirga-zirga a tasakani saboda annobar Korona.
Da yake magana kan wannan, Shugaba Buhari ya ce:
''A yayin tattaunawar mu, mun kuma sake duba jerin dokar hana tafiye-tafiye bisa la’akari da sabbin ka'idojin Korona tare da cire Turkiyya daga cikin jerin haramcin tafiye-tafiye na Najeriya. Tabbas Turkiyya ta sami nasarori masu ban mamaki wajen magance cutar ta Korona.''
Shugaban ya jinjina wa Erdogan da uwargidansa saboda kaddamar da Cibiyar Al'adun Turkiyya a Abuja da kuma bude sabuwar makarantar Sakandaren Gwamnati da aka gyara a Wuse, Abuja, wanda hukumar hadin kai ta Turkiyya ta TIIKA ta gudanar.
A nasa bangaren, Erdogan ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da yin aiki tare da Najeriya a yakin da ake yi da ta'addanci.
Ya bayyana cewa:
‘’A shirye muke mu raba abubuwan da muke ci gaba da fadadawa da Najeriya musamman a fannin masana'antar tsaro da tsaro, wanda duk duniya ta yaba.
''Wannan hankali da muka mayar na yakar ta'addanci, ina fatan 'yan uwanmu maza, 'yan uwanmu mata, da takwarorinmu na Najeriya su ma za su yi hakan."
Shugaban Turkiyya ya gargadi Buhari, ya ce ya kula da masu shirin juyin mulki
A bangaren ganawar, Shugaba Recep Tayyip Erdogan na kasar Turkiyya ya nuna damuwa cewa har yanzu kungiyar 'yan ta'adda ta Fetullah (FETO), wanda ya zarga da yunkurin masa mulkin ba a ranar 15 ga watan Yulin 2016, ya ce su ne a Najeriya.
Erdo spokean ya yi magana ne ranar Laraba a wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da Shugaba Muhammadu Buhari a yayin ziyarar aiki a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban ya gabatar da jawabinsa ne cikin yarensa na Turkiya wanda daya daga cikin jami'ai da ke tawagarsa ya fassara.
Asali: Legit.ng