‘Yan Najeriya na fama da yunwa, talauci da rashin tsaro – Sheikh Dahiru Bauchi ya koka

‘Yan Najeriya na fama da yunwa, talauci da rashin tsaro – Sheikh Dahiru Bauchi ya koka

  • Babban jagoran darikar Tijaniyyah a Najeriya, Sheikh Dahiru Bauchi ya bukaci shugaba Muhammadu Buhari da gwamnoni da su kawo karshen matsalolin tsaro a kasar
  • Malamin ya koka kan cewa al'umman kasar na fama da talauci, rashin tsaro da kuma yunwa
  • Ya yi wannan kiran ne a ranar Talata, 19 ga watan Oktoba

Babban jagoran darikar Tijaniyyah a Najeriya, Sheikh Dahiru Bauchi, ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin jiha da su samo mafita mai dorewa kan matsalolin tsaro a kasar.

Shehin malamin ya yi wannan kiran ne a ranar Talata, 19 ga watan Oktoba a wajen taron Maulidi a jihar Bauchi, jaridar Daily Nigerian ta rahoto.

‘Yan Najeriya na fama da yunwa, talauci da rashin tsaro – Sheikh Dahiru Bauchi ya koka
‘Yan Najeriya na fama da yunwa, talauci da rashin tsaro – Sheikh Dahiru Bauchi ya koka Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Malamin ya ce akwai bukatar shugabannin su yi duk abun da ya dace domin kawo karshen rashin tsaro, da suka hada da ta’addanci, fashi da makami, garkuwa da mutane, da sauransu domin al’ummansu su zauna lafiya.

Kara karanta wannan

Gwamnan Bauchi ya tona asirin wadanda ke hada kai da 'yan ta'adda a jiharsa

A cewarsa, babu wani ci gaba da za a iya samu a kasar da babu zaman lafiya, cewa “idan babu zaman lafiya, Najeriya ba za ta ci gaba ba.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk da tururuwar da ‘yan kungiyar Tijaniyyah suka yi zuwa wajen bikin Maulidin, malamin ya yi korafin cewa rashin tsaro a kasar ya hana mabiyansa da dama zuwa Bauchi domin halartan taron.

Ya ce:

“A baya, mutane kan fito daga wajen Najeriya domin bikin Maulidi amma a yanzu ‘yan tsiraru ne suka zo saboda matsalar rashin tsaro.
“Kwanaki, an farma mutane na a hanyarsu ta komawa gida daga Bauchi zuwa Akungba a jihar Ondo sannan aka kashe fiye da mutane 11 daga cikinsu.”

Ya ci gaba da korafin cewa a yanzu mutane suna tafiya da tsoro a zukatansu saboda rashin tsaro a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Buhari ya fusata da halin 'yan bindiga: Yanzu kam kwanakinku sun kusa karewa

A karshe ya bayyana cewa ‘yan Najeriya na fama da yunwa, talauci da kuma rashin tsaro a kasar, rahoton jaridar Daily Post.

Kisan Jos: Buhari ya girgiza, ko abinci ya kasa ci: Pantami ga Sheikh Dahiru

A wani labarin, mun kawo a baya cewa Ministan Sadarwa da Tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ibrahim Ali Pantami, ya bayyana cewa shugaban Muhamadu ya kasa cin abinci ranar da aka kai hari kan Musulmai a Jos.

A ziyara ta musamman da ya kaiwa Sheikh Dahiru Usman Bauchi, a madadin Buhari, Pantami yace Buhari ya yi matukar bacin rai kan abinda ya faru har abinci ya gaza ci.

Wasu yan bindiga da ake zargin matasan Irigwe ne sun kai wa Musulmai matafiya 90 hari a jihar Plateau ranar Asabar, akalla mutum 22 sun mutu, yan sanda suka tabbatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng