Kisan Jos: Buhari ya girgiza, ko abinci ya kasa ci: Pantami ga Sheikh Dahiru

Kisan Jos: Buhari ya girgiza, ko abinci ya kasa ci: Pantami ga Sheikh Dahiru

  • Ministan Sadarwa ya kai ziyarar jaje ga Sheikh Dahiru Bauchi
  • Akalla mabiyan Dahiru Bauchi 25 matasa Irigwe suka hallaka ranar Asabar
  • Malam Pantami ya bayyana matakan da gwamnati ke dauka kan wannan lamari

Bauchi - Ministan Sadarwa da Tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ibrahim Ali Pantami, ya bayyana cewa shugaban Muhamadu ya kasa cin abinci ranar da aka kai hari kan Musulmai a Jos.

A ziyara ta musamman da ya kaiwa Sheikh Dahiru Usman Bauchi, a madadin Buhari, Pantami yace Buhari ya yi matukar bacin rai kan abinda ya faru har abinci ya gaza ci.

Yace:

"Bayan abin ya faru kuma da gaggawa shi Shugaban kasa tun a ranar ya bada umurni wa jami'an tsaro ayi bincike akai kuma wadanda aka kamasu da laifi a kaisu kotu kuma a hukuntasu."

Kara karanta wannan

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar Ya Yi Magana Kan Kashe Musulmai a Jos

"Ya yi magana da manyan jami'an gwamnati na tsaro a kai. Ya dawo daga tafiya tsakani da Allah da abin ya faru abinci ma yaci gagara yayi."

Yan sanda sun tabbatar da kisan mutum 22 a Jos, sun ce matasan Irigwe ne

Wasu yan bindiga da ake zargin matasan Irigwe ne sun kai wa Musulmai matafiya 90 hari a jihar Plateau ranar Asabar, akalla mutum 22 sun mutu, yan sanda suka tabbatar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Ubah Ogaba, ya bayyana cewa wasu matasa Kirista yan garin Irigwe suka kaiwa Musulman farmaki yayinda suke hanyarsu ta komawa gida bayan halartan taron Zikiri wajen Sheikh Dahiru Bauchi.

Jami'in gwamnatin mai suna Danladi Atu wanda ya ziyarci asibitin da aka kai wadanda suka jikkata yace:

"Mutum 25 aka tabbatar yanzu sun mutu."

Kara karanta wannan

Wannan ba shine farko ba: Izala ta yi martani kan kashe Musulmai da aka yi a Jos

Hakazalika kungiyar Miyetti Allah MACBAN tace ta kirga gawawwaki 25.

Wakilin Miyetti Allah, Malam Nura Abdullahi yace:

"Mun yiwa gawawwaki 25 wanka kuma muna shirin biznesu."

Kisan Jos: Buhari ya girgiza, ko abinci ya kasa ci: Pantami ga Shehu Dahiru
Kisan Jos: Buhari ya girgiza, ko abinci ya kasa ci: Pantami ga Sheikh Dahiru Hoto: Presidency
Asali: UGC

Muna so gwamnati ta dauki mataki ko mu dauki mataki - Dahiru Bauchi

Babban malamin addinin musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bukaci gwamnati ta hukunta wadanda ke da hannu wajen kashe matafiya a Jos.

BBC Hausa ta yi hira da shehin malamin, inda ya bayyana cewa an kure masu hakuri wannan karo, ganin yadda aka dade ana kashe masu mutane a Najeriya.

Shehin yace na farko a biya diyyar wadanda aka kashe ga iyalansu, na biyu a hukunta wadanda suka yi laifin, kuma a dauki dawainiyar wadanda aka ji wa rauni.

Kalli bidiyon:

Asali: Legit.ng

Online view pixel