Rundunar yan sanda ta bankaɗo waɗanda suke da hannu a kisan Sarakuna guda biyu

Rundunar yan sanda ta bankaɗo waɗanda suke da hannu a kisan Sarakuna guda biyu

  • Rundunar yan sanda reshen jihar Imo ta zargi mayaƙan haramtacciyar ƙungiyar IPOB da kisan sarakunan gargajiya biyu a jihar
  • Rahotanni sun bayyana cewa wasu yan bindiga sun budewa sarakunan gargajiya wuta a karamar hukumar Njaba, jihar Imo
  • Kwamishinan yan sandan jihar, Rabiu Hussaini, yace mutanen sun shirya taro amma ba su sanar da yan sanda ba

Imo - Kwamishinan yan sanda na jihar Imo, Rabiu Hussaini, ya zargi haramtacciyar ƙungiyar IPOB da mayaƙan ESN da kisan sarakuna biyu a jihar Imo.

The Nation ta rahoto cewa wasu yan bindiga sun baɗe wa sarakunan gargajiya wuta a ƙaramar hukumar Njaba jihar Imo, mutum biyu suka mutu, ranar Talata.

Kwamishinan ya faɗi haka ne a wata sanarwa da kakakin yan sandan jihar, Michael Abattam, ya fitar ranar Laraba.

Jihar Imo
Rundunar yan sanda ta bankaɗo waɗanda suke da hannu a kisan Sarakuna guda biyu Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yace hukumar yan sanda ta samu rahoto ranar Talata da misalin ƙarfe 3:00 na rana cewa wasu yan bindiga da ake zargin yan IPOB/ESN ne sun farmaki ɗakin taron da shugaban sarakunan Njaba ke ganawa da wasu sarakunan yankin.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Yan sanda sun fara bincike kan yadda jami'an tsaro suka kaɗa kuri'a a zaben APC na tsagin Ganduje

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Kwamishinan yan sandan ya ƙara da cewa nan take ya tura jami'an yan sanda na musamman zuwa yankin bayan samun bayanan abinda ke faruwa.

Bisa rashin sa'a, kafin zuwan yan sandan, tuni maharan suka tsere daga wurin bayan sun hallaka sarakunan gargajiya biyu.

Ya bayyana cewa basaraken Njaba, Hon. Emeka Ihenacho, shine ya gayyaci sarakunan gargajiya 15 zuwa wani taro ba tare da sanar da yan sanda ba.

Yadda lamarin ya faru?

Dailytrust ta rahoto kwamishinan yan sandan yace:

"Suna tsaka da taron ne wasu miyagun yan bindiga da ake zargin mayakan IPIB/ESN ne suka farmakesu, suka buɗe musu wuta kan mai uwa da wabi, daga nan kuma suka gudu."
"Abu mara daɗin ji shine biyu daga cikin sarakunan sun rasa rayuwarsu a harin, yayin da wani ɗaya ya samu raunukan harbi."

Kara karanta wannan

Yadda yan bindiga ke sako mutanen da suka kama ba tare da biyan kudin fansa ba a Zamfara

A wani labarin kuma gwamnatin tarayya tace ko mutum ɗaya sojoji ba su kashe ba a wurin zanga-zangar EndSARS shekarar da ta gabata

Ministan yaɗa labarai, Alhaji Lai Muhammed, yace babu wata shaida ko da ta gawar mutum ɗaya ne, da aka kawo wa gwamnati.

A cewar ministan an kashe sojoji shida da yan sanda sama da 30 a lokacin zanga-zangan amma sam bai dami kowa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262