Hotunan tsohon gwamna ya ɗare kan acaba don gudun kada jirgi ya tashi babu shi a Legas
- Cece-kuce ya yawaita a kafafen sada zumuntar zamani bayan bayyanar hotunan tsohon gwamnan a kan babur
- An ga hotunan tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose a babur din haya ne inda ya ce cunkoso ne ya tunzura shi yin hakan
- Ya bayyana cewa gudun kada jirgin su ya tashi ne ya sa wajibi ya nemi babur din, hakan ya janyo surutai kwarai a Facebook
Jihar Legas - Bayyana hotunan tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose dare-dare a kan babur ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani.
Kamar yadda tsohon gwamnan ya wallafa hotunan a shafin sa na Facebook, sai da ya sauka daga motar sa ne sannan ya dare kan babur a Legas saboda tsabar cunkoso a titin.
Tsohon gwamnan jihar Ekitin ya yi gudun jirgin su ya tashi ya sa ya yi gaggawar neman babur din don ya samu ya isa filin jirgi cikin hanzari.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani ma’abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, Afolabi Oluwatobi ya ce wannan dalilin kadai ya isa a fasa dakatar da babur a jihar.
Tsohon gwamnan kuma babba a jam’iyyar PDP ya wallafa hoton sa da jami’in tsaron da ke kula da lafiyar sa bisa babur a Facebook.
Bayan wallafa hotunan ne ya ce:
“Cinkoson titin Legas ba ya saurara wa kowa. Dole na nemi babur din haya don kada jirgin ya tashi ya barni.”
Daruruwan jama’a su ka dinga tsokaci iri-iri
A ranar Talata, 19 ga watan Oktoba, wannan wallafar ta janyo cece-kuce daga daruruwan mutane, inda su ka dinga tsokaci iri-iri.
Wani Afolabi Oluwatobi cewa ya yi:
“Shiyasa be dace a dakatar da hawa babura ba a jihar Legas. Ya taimaki mutane da dama ta hanyar ayyukan su da sauran su. Ya kamata dai a rage yawan su ne."
Shekara ta 15 kacal, ku bani masauki, ƙaton saurayi ɗan Najeriya ya roƙi jami’an filin jirgi a Ingila
Abdulkareem Adisa Sulyman ta ce:
“Ina tausaya wa dan sandan da zai yi kokarin dakatar da ku. Zan so ace wani jami’in LASTMA zai kama ku da an kwashi ‘yan kallo. Gaskiya ka na sa rayuwar ka a hadari.”
Yusuf Adebanjo kuwa cewa ya yi:
“Kaga wanda ya san abinda ya ke yi. Ni kai na na sha dandana kuda ta, bayan na sa kaya masu kyau da turare mai tsada, haka zan sa da kai in taka da kafafuna idan na ga jirgi zai tashi ya bar ni. Dole ne ka yi amfani da kwakwalwar ka wurin yin abinda ya dace a Legas.”
Da sauran tsokaci iri-iri daga mutane daban-daban, wasu su na yaba ma sa wasu kuma su na ganin ya sa rayuwar sa a hatsari.
Asali: Legit.ng