'Yan sanda sun yi ram da baƙin haure 2 dauke da abubuwa masu fashewa cikin jakunkuna

'Yan sanda sun yi ram da baƙin haure 2 dauke da abubuwa masu fashewa cikin jakunkuna

  • ‘Yan sanda sun kama wasu mutane 2 daga kasar waje da abubuwa masu fashewa a yankin Niger Delta
  • Jami’in hulda da jama’an yankin, SP Odiko Mcdon ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Talata
  • A cewar Mcdon, jami’an tsaron sun kama su ne yayin sintiri a daidai babban titin Okobo-Iron

Jihar Akwa-Ibom - Rundunar ‘yan sandan yankin Akwa-Ibom sun samu nasarar damkar wasu ‘yan kasar waje 2 da abubuwa masu fashewa kamar yadda ya zo a rahoton Channels TV.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Odiko Mcdon ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai a ranar Talata a hedkwatar ‘yan sanda da ke Uyo, babban birnin jihar.

‘Yan sanda sun yi ram da baƙin haure 2 da abubuwa masu fashewa a Akwa Ibom
Jami'an yan sandan Nigeria. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Jaridar ta ruwaito cewa wadanda ake zargin sun hada da Adede De Black, Fombutu da Benard Mfam daga karamar hukumar Ikom da ke jihar Cross River.

Kara karanta wannan

Kaduna: Jami'an tsaro sun kashe 'yan bindiga da dama, sun banka wa sansaninsu wuta

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce jami’an sintirin AIG na bakin iyaka ne su ka damki wadanda ake zargin akan babban titin Okobo-Oron.

Bayan dakatar da su, an bincike su tsaf sannan aka ga jakunkuna 2 na abubuwa masu fashewa, layoyi da miyagun makamai.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya samar da sabbin tsare-tsare

‘Yan sandan sun ce sun samu nasarar ne sakamakon yadda kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Amegieme Andrewa ya samar da sabbin tsare-tsare don yin garanbawul akan matsalolin tsaro.

Sannan Kakakin rundunar ya tabbatar wa da mazauna yankin cewa rundunar ‘yan sanda za ta ci gaba da kulawa da rayuka da dukiyoyin su.

Har ila yau, rundunar ‘yan sanda ta yaba da masu masana’antun yankin bisa yadda su ka jajirce wurin saukaka samuwar ayyukan yi a Akwa Ibom.

Kaduna: Jami'an tsaro sun kashe 'yan bindiga da dama, sun banka wa sansaninsu wuta

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya tana biyan malaman jami’a N6, 000 rak a matsayin albashin karshen wata

A wani rahoton kun ji cewa jami’an tsaro sun harbe ‘yan bindiga 10 a Kwanan Bataru, wajen Fatika da ke karkashin karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna.

Sannan har maboyar ‘yan bindigar ma ba ta tsira ba, sai da jami’an tsaron su ka banka ma ta wuta.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164