Yadda miliyoyin kudi su ka ceto Sarki guda daga hannun miyagun ‘Yan bindiga da kyar

Yadda miliyoyin kudi su ka ceto Sarki guda daga hannun miyagun ‘Yan bindiga da kyar

  • Sarkin Fulanin Bungudu ya shafe sama da wata daya a hannun ‘yan bindiga
  • Duk da an biya fansar N20m, miyagun ba su kyale Alhaji Hassan Attahiru ba
  • Sai da aka hada da 'Yan Miyetti Allah da karin kudi kafin a fito da Basaraken

Zamfara - Miyagun ‘yan bindiga sun karbi makudan miliyoyin kudi a matsayin fansa kafin su fito da Mai martaba Sarkin Fulanin Bungudu, Hassan Attahiru.

Premium Times ta fitar da rahoto da ya bayyana cewa ‘yanuwa da iyalin Mai martaban sun biya wasu karin kudi a kan Naira miliyan 20 da suka fara biya.

Da farko an damka wa ‘yan bindigan da suka sace Mai martaban a hanyar Abuja Naira miliiyan 20. Amma hakan bai sa ya fito bayan sama da wata daya ba.

Kara karanta wannan

Zagayen Maulidi: Wahala ta kashe mutum daya, wasu goma sun sume a Abuja

An toshe hanyoyin sadarwa

Bayan gwamnati ta toshe kafofin sadarwa domin a kawo karshen satar mutane da ake yi, na-kusa da Sarki Attahiru sun samu cikas wajen magana da miyagun.

Wannan mataki da aka dauko ya jawo aka bata lokaci kafin a iya fito da Sarkin na Bungudu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sarkin Bungudu
Sarkin da aka sace a Zamfara Hoto: Legit.ng Hausa
Asali: Original

Jaridar tace ‘yan bindigan sun koma wuraren da za su iya magana ta salula da ‘yanuwan Sarkin, har suka yi nasarar gabatar da karin bukatunsu a wajensu.

Amma duk da wayoyin da aka rika yi da ‘yan bindigan, ‘yanuuwan mai martaba, ba su ji muryarsa ba saboda ba za a iya waya a inda yake daure ba.

N20m tayi kadan

‘Yan bindigan sun nemi a kawo masu Naira miliyan 100 a lokacin da aka fara tattauna wa. Bayan sun karbi Naira miliyan 20, sai suka cigaba da tsare Sarkin.

Kara karanta wannan

Bincike: Yadda Ministan Buhari yake amfani da kujerarsa yana yin abin da ya ga dama a mulki

Majiyar tace Miyetti Allah ta shiga lamarin, amma sai da aka kara biyan wasu kudin fansa. An kai kudin ne wani kungurmin jeji a gaba da Rigachikun, Kaduna.

“A karo na biyun ma an bada kudi masu yawa, ba zan iya cewa nawa ba ne. Bayan kungiyar Miyetti Allah da wasu sun sa baki, sai aka fito da Sarkin.”
“Bayan an sake shi, ya yi tafiyar sa’o’i uku a jeji kafin ya kai inda aka je aka dauko shi a babur, daga nan ya shiga motocin da suke jiran shi” - Majiya

'Yanuwa da abokan arziki sun bar wa Allah

Kwanaki kun ji yadda ‘yanuwa, talakawa da abokan arziki sun shiga wani yanayi tun bayan da ‘yan bindiga suka dauke Sarkin Bungudu, Hassan Attahiru.

Bayan an biya kudin fansa sai aka daina jin duriyar 'yan bindigan. Hakan ya sa iyalai da abokan arziki suka fara tunanin Mai martaban ya mutu ne a tsare.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun sace tagwayen ‘yan mata, Direba da wasu Dogaran Sarki a Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng